Har yanzu ’yan Najeriya suna tare da Buhari – Barista Hawaja
Barista Yusuf Gambo Hawaja shi ne Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Filato, a tattaunawarsa da wakilinmu ya ce duk da halin matsin da ake fama da shi a kasar nan, har yanzu ’yan Najeriya suna tare da Shugaban kasa Buhari. Kuma ya ce tunda ake kafa gwamnati a jihar, ba a taba samun gwamnatin […]
Barista Yusuf Gambo Hawaja shi ne Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Filato, a tattaunawarsa da wakilinmu ya ce duk da halin matsin da ake fama da shi a kasar nan, har yanzu ’yan Najeriya suna tare da Shugaban kasa Buhari. Kuma ya ce tunda ake kafa gwamnati a jihar, ba a taba samun gwamnatin da take tafiya da al’ummar Jos kamar gwamnatin Barista Simon Lalong ba:
Aminiya: Wadanne nasarori ne kake ganin gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu a cikin shekara daya na mulkinta?
Barista Hawaja: Nasara ta farko da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta samu a shekara daya shi ne zaman lafiya, wanda idan babu shi ba za a iya komai ba. Haka ta samu nasarar hada kan al’ummar kasar nan. Domin kafin zuwan wannan gwamnati za ka ga mabiya addinai suna fada da juna, wannan kabila da waccan suna fada, amma yanzu wannan abu ya ragu sosai, duk dai bai kare duka ba. Bayan haka gwamnatin ta samu nasarar rage sace kudin gwamnati, shi ya sa wadanda suka saba da satar suke ta zage-zage, sannan ta samu nasarar karbo wasu kudin gwamnati da aka sace. Bugu da kari a zamaninta martabar Najeriya ta dawo a idon kasashen duniya, wadannan kadan ne daga cikin nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu a cikin shekara daya.
Aminiya: To me za ka ce kan koke-koken da ’yan Najeriya ke yi, kan halin matsin rayuwa da tsadar kayan masarufi a lokacin gwamnatin?
Barista Hawaja: Gaskiya ne ana cikin wahala da matsi a kasar nan, amma ana yin gyara ne kuma da yardar Allah da hakurin da mutane suke yi, kasar nan za ta gyaru. Amma tabbas ana cikin wahala, akwai wahalar tattalin arziki akwai ta zamantakewa akwai ta kiwon lafiya da sauransu. Amma dama an riga an lalata wadannan abubuwa ne kafin zuwan wannan gwamnati, kuma babu yadda za a yi a ce a lokaci daya, za ta iya magance matsalolin. Dole sai mun yi hakuri mun bi hanyoyin gyara baki dayanmu. Duk wahalhalun da muke ciki tsiyatakun Jam’iyyar PDP ne, kuma gwamnatin Shugaba Buhari tana kokarin magance matsalolin, gwamnatin nan ba za ta dauki kudi haka kawai ta bai wa mutum ba tare da ya yi wani aiki ba. Wannan gwamnati za ta taimaki aikin gona da harkokin ilimi da kiwon lafiya da gina hanyoyin mota, amma dole sai mun kara hakkuri. Idan aka ce za a ci gaba da yin abubuwan da PDP suka yi, na raba wa mutane kudi haka kawai, za a shiga matsalar da tafi ta baya. PDP sun lalata kasar nan ya kai har shugabanni suna tsoron su fada wa mutane gaskiya. To yanzu gaskiyar ake fada wa mutane, idan ka ce babu kudi a ce ka cika kuka, idan ka ce idan za a karbi kudi a bi ka’ida, a ce ka cika matsawa. Wani ma ba ya aikin gwamnati ba ya kwangila, amma sai ya ce gwamnati ta ki ba shi kudi. A da ana tsoron mutum kada ya zagi gwamnati ko Shugaban kasa ko Gwamna sai a debo kudi kamar Naira miliyan 50 a ba shi, don kada ya je ya yi magana. Yanzu an dakatar da wannan, idan za ka yi zaginka ka je ka yi, amma ba za a dauki kudin mutane a ba ka ba. Duk makarkashiyar da ake yi wa gwamnatin Buhari ba za ta kai ga nasara ba, saboda idan aka lura har yanzu mutanen Najeriya suna son Buhari suna tare da shi, sun yarda da manufofinsa, suna ba shi uzuri kuma suna yi masa addu’a. Masu sukar gwamnatin Buhari yawancinsu masu laifuffuka ne da suka saba sace kudin gwamnati, yanzu kuma babu dama an hana su.
Aminiya: Me kake ganin ya kamata gwamnati ta yi kan ’yan tawayen yankin Neja-Delta da suke fasa bututun mai da gas?
Barista Hawaja: Abin da yake faruwa yanzu a yankin Neja-Delta abin takaici ne, amma a ra’ayina a tattauna da ’yan tawayen tukuna. Domin a yankin akwai wadanda ba sa goyon bayan abin da ke faruwa. Ai ko ’yan Boko Haram sai da aka ba su dama su zo a tattauna, amma suka ki suka ci gaba da barnarsu, yau ina makomarsu? Saboda haka a tattauna su ajiye makamansu, idan suka ki tattaunawa da gwamnati abin da zai same su ba za su ji dadi ba, domin Najeriya ta fi karfinsu, babu wani tsagera da zai ce zai yi
abin da ya ga dama a Najeriya.
Aminiya: A nan Jihar Filato wadanne nasarori gwamnatinku ta samu a shekarar?
Barista Hawaja: Bambancin gwamnatin Shugaba Buhari da gwamnatin Barista Simon Lalong ba su da yawa. Domin idan ka lura kafin zuwan rikicin Boko Haram, Jihar Filato ta fi kowace jiha zubar da jini a Najeriya, kuma da zuwan gwamnatin Lalong ga yadda jihar ta zama kan zaman lafiya da kwanciyar hankali. Domin abin da Gwamna Lalong ya fara sanyawa a gaba, shi ne maganar zaman lafiya. Kuma Allah Ya taimaka an samu zaman lafiya a jihar. Yanzu a Jihar Filato kowa yana shiga duk inda ya ga dama ba tare da tsoro ko fargaba ba. Ba bangaren da Musulmi ba ya shiga, haka babu bangaren da Kirista ba ya shiga, an samu gagarumin hadin kai a jihar sakamakon zuwan gwamnatin Lalong. Sannan lokacin da gwamnatin Lalong ta zo, ta tarar da ba a aikin gwamnati kwata-kwata a jihar, wato ma’aikata suna yajin aiki saboda sun yi watanni ba a biyansu albashi, inda ya kira shugabannin kwadago ya zauna da su ya roke su aka koma aiki, kuma aka fara biyan albashi. Kuma gwamnatin ta ci gaba da gudanar da ayyukan raya kasa da gwamnatin da ta gabata ta faro. Misali ta ci gaba aikin babbar hanyar nan da ta tashi daga Jos zuwa bukur da Jami’ar Jihar Filato da take Bokkos da aka kafa shekara 10 da suka gabata, wadda tunda aka kafa ta ba ta taba yaye dalibanta ba. Yanzu mun samu amincewar Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa (NUC), in Allah Ya yarda za a fara yaye daliban jami’ar bana. Gwamnatin Lalong ta zo ta samu sama da shekaru 10 ba a bayar da takardar shaidar mallakar fili a Ma’aikatar kasa da Safiyo ta jihar, amma yanzu Gwamna Lalong ya bayar da makudan kudi an gyara wannan ma’aikata an fara bayar da takardar shaidar mallakar filin. Maganar hanyoyi misali a cikin garin Jos a da mutanen Jos abin tausayi ne amma da Gwamna Lalong ya zo ya gyara hanyoyin cikin garin Jos, yanzu hanyoyin da ba a gyara ba a cikin garin Jos ba su da yawa. Wadannan abubuwa da muka yi, ya sanya ’yan adawa sun rasa yadda za su yi da mu, domin ba su son a ce mun ci nasara. Kuma mun zo a lokacin rashin kudi domin jami’an gwamnatin da ta gabata a jihar nan sun yi kuruciyar bera ta hanyar sace kudin jihar. Kwanan nan muka gano mutum daya yana daukar albashin malamai 1,832, gwamnatin baya tana kallon irin wadannan abubuwa suna faruwa amma babu abin da ta yi. Yanzu muna gyaran makarantu da asibitoci, kuma mun hada kai da kamfanonin kasashen waje. A kwanakin baya Gwamna Lalong ya je kasar China ya gana da wasu kamfanoni a can, kafin ya dawo Najeriya har wasu kamfanonin hakar ma’adanai sun iso Jihar Filato daga China.
Aminiya: A matsayinka na Bahaushe kuma wanda ya fito daga karamar Hukumar Jos ta Arewa, yaya za ka kwatata yadda gwamnatin Lalong take tafiya da mutanenku da gwamnatocin da suka gabata?
Barista Hawaja: To, na farko dai a da ba a yi da mu, domin gwamnatocin jihar nan da suka gabata, ba su san ma muna raye ba. Bayan mu ne kashin bayan tattalin arzikin jihar nan, amma duk da haka ba sa yin komai da mu. Amma bayan da Gwamna Lalong ya ci zabe, bai manta da karamcin da mutanen Jos suka yi masa ba, mun yi alkawura da shi kamar guda tara, ina tabbatar maka zuwa yanzu ya cika alkawura shida zuwa bakwai. Domin ka ga dai ya yi mana alkawarin gyara Babbar Kasuwar Jos da ta kone, wannan kasuwa ta Jihar Filato ce, amma saboda wani dalili na gwamnatin da ta gabata, ta ki ta gyara kasuwar. A yanzu gwamnatin Lalong ta gayyato wasu kamfanoni da ake son kulla yarjejeniyar gyara wannan kasuwa da su. Gwamna Lalong ya ba mu mukaman da ba a taba ba mu ba a jihar nan, domin kamar ni kaina ya ba ni Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar, bayan haka ya ba mu kwamishina. Mun kai shekara 10 gwamnati ba ta haka lambatu ba a garin Jos, amma Gwamna Lalong ya zo ya yi mana gyare gyaren hanyoyi, ya yi mana makabarta kuma ya dawo da Sakatariyar karamar Hukumar Jos ta Arewa zuwa wurin da take, wadda aka dage ta saboda a nesanta mu da gwamnati. Haka ya yi mana gyare-gyaren makarantu da sauran abubuwa. Don haka muna yi masa godiya kuma muna yi masa addu’a Allah Ya taimake shi ya ba shi nasara kan kudirorin da ya sanya a gaba, na bunkasa jihar nan.