Harajin da ake karɓa a Najeriya ya yi kaɗan — Bill Gates
Attajirin ya ce akwai buƙatar ƙara kuɗin haraji domin inganta harkar kiwon lafiya da ilimi.
Fitaccen Attajirin nan na Duniya, Bill Gates, ya bayyana cewar harajin da Najeriya ke karɓa bai taka kara ya karya ba.
A cewarsa rashin samun isasshen harajin na hana samun tallafawa muhimman bangarori kamar kiwon lafiya da ilimi.
Ya bayyana wannan ne yayin taron matasa kan abinci a Abuja.
Gates, ya yi nuni da cewa dole ne gwamnati ta ɓullo da manufofi domin samar da ingantacciyar hanyar kiwon lafiya.
Ya kuma jaddada buƙatar samun ƙaruwar kuɗaɗen haraji don tallafawa waɗannan ayyuka.
Jawabinsa, ya biyo bayan tayin da Shugaban Kwamitin Farko na Shugaban Ƙasa ka Sake Fasalin Haraji, Taiwo Oyedele, ya yi na ƙara kuɗin harajin kayayyaki daga kashi 7.5 zuwa kashi 10 nan da 2025.
Oyedele, ya nuna cewa harajin Najeriya ya yi ƙasa sosai, kuma gwamnati tana shirin rage harajin kamfanoni tare da haɗe wasu harajin.
Gates, ya kuma yi nuni kan muhimmancin tabbatar da shirye-shiryen kiwon lafiya su zama abin dogaro da kuma inganta su.
Ya ce akwai buƙatar kula da cibiyoyin kiwon lafiya yadda ya kamata, tare da samar da ma’aikata da ƙwararru, wanda zai taimaka wajen inganta lafiyar jama’a, wanda hakan zai sa ’yan Najeriya su ƙara tallafa wa kuɗaɗen da ake buƙata a ɓangaren kiwon lafiya da ilimi.
Bugu da ƙari, Oyedele ya bayyana cewa waɗannan shawarwarin na sake fasalin haraji an tsara su ne don samar da tsarin kuɗi, wanda zai rage yawan haraji ga mutane da kamfanoni.
Ya ce hakan zai tabbatar da cewa gwamnati tana samun isasshen kuɗaɗen shiga don biyan buƙatun ƙasa.