Harajin tsaron Intanet: ‘Gwamnatin Tinubu ba ta da tausayi’

Dole ne gwamnatin Tinubu ta gaggauta janye dokar da Bankin CBN ya bayar.

Harajin tsaron Intanet: ‘Gwamnatin Tinubu ba ta da tausayi’

Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) da Jam’iyyar PRP da kungiyoyin fararen hula (CSOs) da kwararru da kuma talakwan Nijeriya sun sa kafa sun yi fatali da sabon harajin yaki da zamba ta Intanet da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bullo da shi, inda suka ce gwamnatin Tinubu ba ta da tausayi.

Bangarorin sun ce sabon harajin karin wahala ne a kan ’yan Nijeriya da suke cikin kunci kuma zai yi illa ga harkokin kasuwanci.

Wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da Kungiyar Kare ’Yancin Rayuwa da Tattalin Arziki da Tabbatar da Amana (SERAP) ta ba Shugaba Bola Tinubu zuwa yau Juma’a ya umarci Bankin CBN ya janye wannan umarni ko su hadu a kotu.

Bankin CBN ya umarci bankunan kasar nan su fara cire kaso 0.5 na harajin tsaron Intanet a kan huldar tura kudi ta waya ko Intanet.

A wata takarda dauke da sa hannun Daraktan Kula da Tsarin Biyan Kudade, Chibuzor Efobi da Daraktan Tsare-Tsaren Kudi da Dokoki na babban bankin ta ce, za a fara aiwatar da cire harajin ne cikin mako biyu masu zuwa.

Takardar ta ce wannan karin bayani ne a kan wasikar da aka fitar a ranar 25 ga Yunin, 2018 mai lamba (Ref:BPS/DIR/ GEN/LAB/CIR/05/008) da ta ranar 5 ga Oktoban, 2018 mai lamba (Ref:BSD/DIR/GEN/ LAB/11/023), kan aiki da Dokar Yaki da Satar kudi ta Intanet ta 2015.

A cewar Bankin CBN, cirewa da karbar harajin tsaron Intanet ya biyo bayan kafa Dokar Yaki da kuma Hana Sata ta Intanet ta Shekarar 2024 ne.

‘Karin jerin haraji’

Sabon harajin ya zo ne ’yan kwanaki bayan bankunan kasuwanci sun dawo da biyan haraji a kan kudin masu yawa da aka kai ajiya a banki daga daidaikun mutane da kungiyoyi ko kamfanoni.

Aminiya ta gano kudin da ake cirewa na kaso biyu da kaso uku a kan ajiyar da ta kai Naira dubu 500 a asusun daidaikun mutane da miliyan 3 a asusun kungiyoyi ko kamfanoni an dakatar da shi tsawon wata shida kafin a dawo da shi.

Wannan kari ne a kan sauran kudaden da ake cirewa a harkokin kudi a bankuna kamar harajin tura kudi ta waya ko Intanet (EMTL) da kudin da ake cira kan aika sakon waya (SMS) da sauransu.

Kudin EMTL da ake cira shi ne Naira 50 idan aka tura ta Intanet ko aka karba yayin tura kudi a bankin kasuwanci ko cibiyar kudi ko kowane asusu da kudin ya kai Naira 10,000 zuwa sama.

Sai dai Bankin CBN ya umarci bankunan kasuwancin su dakatar da cirar kudi a kudin da aka kai ajiye har zuwa ranar 30 ga Satumban 2024.

A farkon wannan wata Gwamnatin Tarayya ta umarci bankuna su hanzarta cire kaso .0375 na harajin fito kan duk kudin rancen gina gida da lamunin na gwamnati.

Wadannan su ne basussukan da cibiyoyin kudi suka ba daidaikun mutane ko kamfanoni su sayi gida su biya bashin daga baya na wani lokaci tare da kudin ruwa, yayin da lamuni kuma bashi ne da gwamnatoci ko masu zuba jari da kamfanoni ko wasu cibiyoyi suke bayarwa don kafa jari.

Sabon harajin tsaro na Intanet an kara shi ne a kan sauran harajojin da ake karba daga daidaikun mutane da kamfanonin da suke hada-hada da cibiyoyin kudi, lamarin da ya sa masu ruwada-tsaki da kwararru suka ce sabon harajin bai dace ba, yayin da masana tattalin arziki suka ce harajin zai sa mutane su guje wa hulda da bankuna.

Harajin karin wahala ne da kunci ga ma’aikata – NLC

Wata sanarwa daga Shugaban Kungiyar NLC ta Kasa, Joe Ajaero ta ca harajin wani tsari ne na dada cutar da jama’a na gwamnati a daidai lokacin da ake fama da kuncin tattalin arziki.

“Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC), tana matukar la’antar sabon umarnin na Bankin CBN, na a biya harajin tsaron Intanet na kaso .05 kan tura kudi ta waya ko Intanet.

“Wannan haraji za da za a aiwatar ta hanyar cire kudi a hadahadar da aka yi, wani karin wahala ne a kan ma’aikatan Nijeriya.

“A wata takarda da Bankin CBN ya fitar an umarci bankuna su fara cire wannan kudi a mako biyu masu zuwa.

“Wannan yunkuri an ce an yi ne don tabbatar da hana satar kudi ta Intanet, ba wani abu ba ne face kara kuntata wa jama’a da tuni suke fama da wahala,” in ji NLC.

Da yake magana kan batun Daraktan Kungiyar Action Aid na Nijeriya (AAN), Mista Andrew Mamedu ya ce, baya ga tsoron ko za a tabbatar ana amfani da kudaden bisa adalci, akwai kuma babbar damuwa kan karin wahala da wannan tsari zai kara wa talakan da tuni yake cikin kunci.

“Akwai tsoron cewa bankuna da kamfanonin tarho za su dora nauyin biyan wannan haraji ne a kan abokan huldarsu, ma’ana su dora nauyin biyan harajin ga jama’a.

“Wannan ba kawai zai kara wahala a kan jama’a kadai ba ne, zai bukaci amsar tambayar ko za a yi adalci wajen kula da amanar dukiyar da za a tara da sunan yaki da hana sata ta Intanet din.

“Yana da muhimmanci a tabbatar da an samar da tsarin da zai hana bankuna da kamfanonin tarho amfani da wannan tsari wajen dora wa abokan huldarsu nauyin biyan kudaden da su ya kamata su biya.

“Dokar ta umarci Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkokin Tsaro ya tabbatar da adana bayanan asusun kudaden tare da tabbatar ana bincikarsu ta hannun Odita Janar na Tarayya.

“Yayin da wadannan matakai za su inganta tabbatar da amana, abin tsoron shi ne batun cikakken sa-ido da kare dukiyar daga almubazzaranci ko karkatar da ita,” in ji shi.

Mutane za su bar ajiya a bankuna — Masana

Wani masani tattalin arziki Farfesa Ndubisi Nwokoma ya ce sabon harajin zai sa jama’a da dama su daina kai ajiya a bankuna.

Ya ce, “Jama’a na fama da wahala suna neman abin da za su ci, amma yanzu an kara musu wani sabon harajin, na lura suna son samun karin kudi, amma jama’ar da kuke son samun kudin daga wajensu ba su da wata hanya ta samun kudin da zai iya rike su, kuma hakan zai sa mutane da dama su daina ajiya a bankuna.”

Ya ce idan har ajiyar ta kasance matsala a banki, dole mutum ya koma yin mu’amala da kudi kai-tsaye.

Ya ba da misali cewa idan mutum zai biya kudin kayan da ya saya na Naira dubu 10, wanda za ka biya kudin ba zai samu dubu 10 a asusunsa na banki ba, sai dai kasa da haka.

Don haka manyan ’yan kasuwa na cikin matsala, haka idan ka ki sa kudinka a banki nan ma wata matsalar ce, hakan zai sa dole mutane su lalubo hanyoyin da za su ajiye kudadensu, wanda hakan wata babbar barazana ce, don haka ina ganin wannan tsari ba ya da wata fa’ida.

Dokta Muda Yusuf Babban Shugaban Cibiyar Inganta Harkokin Kasuwanci Mai Zaman Kanta (CPPE) ya ce sabon harajin babban abin damuwa ne.

Ya ce “Harkokin kasuwanci da al’umma har yanzu ba su gama farfadowa daga matsin tattalin arziki da aka jefa su a ciki ba.

Matsalar hauhawar farashi da gurguncewar harkokin kasuwanci, duk ba a gama fita daga cikinsu ba, don haka wannan ba lokaci ne na karawa al’umma wani sabon haraji ba.

Dokta Muda ya kara da cewa, tuni ’yan kasuwa ke fama da tarin haraji irin daban-daban, don haka ya kamata hukumomi su duba lamarin.

Wani masanin kimiyya Mista Oni Toluwa cewa ya yi wannan wani nau’i ne na zaluntar jama’a, ta yaya gwamnati za ta dauki irin wannan mataki, wannan tamkar danniya ce gwamnati take yi wa al’umma.

Ya ce babu wani tsari guda da talaka ke amfana da shi, illa kuncin rayuwa, kuma yanzu ga wani haraji na tsaron Intanet. Shin da gaske ne gwamnati ba ’yar damfara ba ce? Duk harajin da ake samu bai wadatar ba, wannan bai dace ba.

SERAP ta ba Tinubu sa’o’i 48

Kungiyar SERAP ta bukaci Shugaban Kasa Bola Tinubu ya umarci Bankin CBN ya hamzarta janye harajin, domin hakan ya saba wa Kundin Tsarin Mulki kan tauye hakkin dan Adam.

Haka SERAP ta bukaci ya dakatar da Malam Nuhu Ribadu da ofishinsa daga kaddamar da Sashi na 44 da sauran batutuwa da suka shafi aikita laifi ta Intanet, domin aiwatar da hakan ya saba wa dokar hakkin dan Adam da kare mutuncinsa.

Sanarwar da Mataimakin Daraktan Kungiyar Mista Kolawole Oluwadare ya sa wa hannu, ta bai Gwamnatin Tinubu wa’adin sa’o’i 48 ta janye harajin ko ta kai batun kotu.

Sanarwar ta ce, “Dole ne gwamnatin Tinubu ta gaggauta janye dokar da Bankin CBN ya bayar na aiwatar da Sashe na 44 na dokar aikata laifuffuka ta Intanet ta shekarar 2024, wadda ta dora wa ’yan Nijeriya wannan haraji.

Tsarin rashin tausayi ne — PRP

Ita ma Jam’iyyar Ceton Al’umma (PRP) ta yi matukar Allah wadai da sabon umarnin. A wata sanarwa da Mukaddashin Babban Sakataren Jam’iyyar Kwamared Mohammed Ishak ya fitar, ta bayyana harajin da “Wani tsari na rashin tausayi na Gwamnatin Bola Tinubu.

“Wannan tsari na rashin ya kamata da ya zo a irin wannan lokaci kuma ake sa ran zai fara aiki nan da mako biyu, babu abin da zai yi face kara kuntata wa ’yan Nijeriya da suke fama da kuka kan matsalolin tattalin arziki a yanzu.

“Dora wa mutane wannan haraji zai yi matukar cutar da masu rauni a cikin al’umma ciki har da daidaikun mutane masu kwazo da iyalai da kananan ’yan kasuwa da masu sana’o’i.

“Babban abin damuwa shi ne za a mika kudin da za a karba ne ga Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkokin Tsaro ba tare da an ajiye wani cikakken tsarin kiyaye gaskiya da amana kan yadda za a yi amfani da su ba,” in ji sanarwar.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta