Harbe ni in za ka iya: Amaechi ga Kwamshinan ’Yan sanda

Gwamnan Jihar Ribas Cif Rotimi Chibuike Amaechi ya nanata cewa zai jagoranci zanga-zangar da aka shirya a jihar kuma ya kalubalanci Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Mista Mbu Joseph Mbu kan ya harbe shi idan zai iya.Wannan kalubale na Amaechi ya zo ne a daidai lokacin da shugabannin kananan hukumomin jihar suka zargi jagoran ’yan sandan […]

Harbe ni in za ka iya: Amaechi ga Kwamshinan ’Yan sanda
Harbe ni in za ka iya: Amaechi ga Kwamshinan ’Yan sanda

Gwamnan Jihar Ribas Cif Rotimi Chibuike Amaechi ya nanata cewa zai jagoranci zanga-zangar da aka shirya a jihar kuma ya kalubalanci Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Mista Mbu Joseph Mbu kan ya harbe shi idan zai iya.
Wannan kalubale na Amaechi ya zo ne a daidai lokacin da shugabannin kananan hukumomin jihar suka zargi jagoran ’yan sandan da jefa harkokin tsaron jihar cikin hadari saboda siyasa.
Gwamnan ya fadi haka ne a Fatakwal a ranar Talatar da ta gabata lokacin da al’ummar yankin Orashi da ke jihar a karkashin jagorancin Wilson Ake suka kai masa ziyarar goyon baya, inda ya ce zai ki bin umarnin Kwamshinan ’Yan sandan na kada ya shiga zanga-zangar. “Na gaya wa Kwamishinan ’Yan sandan ya shirya domin harbina. Zan jagoranci zanga-zangar nuna kyama gare shi. Muna da goyon bayan sarakunanmu kuma muna jiran mutanenmu da suke wajen jihar da kasa. Za mu gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadi kan abin da Gwamnatin Tarayya da Kwamishinan ’Yan sandan suke yi a Jihar Ribas. Mun shaida wa sarakuna su zauna cikin shiri. Lokacin da muka ajiye rana, muka samu muttanenmu daga kasashen waje da kuma Najeriya da za su hade da mu, za mu bayyana ranar da za a yi zanga-zangar,” inji shi.
Gwamnan ya ce wasu daga cikin matsalolin da suke fuskanta su ne, na ’yan siyasar jihar da ke zaune a Abuja wadanda wasu mutane daga wajen jihar suka yi garkuwa da su domin jawo fitina a Ribas. Ya ce wata matsalar ita ce kiyawar da gwamnatin jihar ta yi na ta bar rijiyoyin mai mallakar jihar ga jihohin makwabta su karbe su.
Ya ce, “Sun kwace mana rijiyoyin mai a Etche, sun kwace mana rijiyoyin mai daga Kalabari, sun kwace mana rijiyoyin mai a Andoni yanzu suna gwagwagwa kan sai sun kwace wadanda suke Ogba/Egbema/Ndoni. Kullum muna asarar rijiyyoyin manmu. Idan na yi magana sai su ce na cika taurin kai, to, amma wajibi ne mu kare hakkokinmu. Muna da ’yancin zama ’Yan Najeriya. Wasu daga cikin masalolin da muke fuskanta suna faruwa ne saboda muna gwagwarmayar kare rijiyoyin manmu ne.”