Harbin dalibai ya haddasa rufe Jami’ar Jos
A ranar Talatar da ta gabata ce hukumar gudanarwar Jami’ar Jos ta rufe jami’ar a sakamakon tarzomar da dalibai suka tada, suna kalubalantar karin kudin makaranta da aka yi musu. A sakamakon haka jami’an tsaro suka bude wuta, wanda ya haddasa raunata dalibai 11 na jami’ar.Magatakardar jami’ar, Jilli Dandam ne ya fitar da wata takardar […]
A ranar Talatar da ta gabata ce hukumar gudanarwar Jami’ar Jos ta rufe jami’ar a sakamakon tarzomar da dalibai suka tada, suna kalubalantar karin kudin makaranta da aka yi musu. A sakamakon haka jami’an tsaro suka bude wuta, wanda ya haddasa raunata dalibai 11 na jami’ar.
Magatakardar jami’ar, Jilli Dandam ne ya fitar da wata takardar sanarwa, inda ya nemi dalibai da su bar harabar jami’ar da nufin dakile ci gaban hargitsin, inda daga bisani aka rufe jami’ar har zuwa wani lokaci nan gaba.
Jami’in hulda da jama’a na kungiyar daliban jami’ar, Longgun Dakwon ya shaida wa wakilanmu cewa sojoji ne suka mamaye harabar jami’ar suka fara harbe-harbe kuma suka kama wasu daga cikin daliban. A nasa bangaren, jami’in hulda da jama’a na Rundunar Tsaro Ta Musamman, Kyaftin Ikedichi Iweha ya musanta cewa akwai hannun sojoji cikin harbe-harben da aka yi a jami’ar amma ya tabbatar da cewa lallai kam akwai dalibai hudu da ke amsar magani a harabarsu. Ya kara da cewa jami’ansu hudu ma sun samu raunuka a sakamakon yadda bata-gari suka shiga cikin tarzomar. Ya ce jami’an tsaro ne ma suka tallafi daliban da suka samu raunuka, suka kai su wajensu, inda ake ba su magani kuma yanayin jikinsu yana samun sauki a halin da ake ciki.
“Babu wani jami’inmu da ya yi wani harbi. A ranar farko da tarzomar ta faru, dalibai sun rika watsa mana ruwa kuma suna jifar mu amma duk da haka ba mu mayar da martani ba. A yau kuma mun ga cewa akwai bukatar karin jami’an tsaro, don haka sauran jami’an suka shigo cikin batun.” Inji Kyaftin Iweha.
Ya ja hankalin daliban da su guji take hakkin masu amfani da hanyoyi, inda ya jaddada cewa kayayyakin jami’ar na fuskantar barana, a sakamakon yadda daliban suka bari bata-gari suka amshe ragamar zanga-zangar.