‘Harbin masu zanga-zanga yana tuna min lokacin mulkin kama karya’

Wajibi ne a hukunta masu fakewa da zanga-zangar suna sacewa da barnata dukiyar jama’a.

‘Harbin masu zanga-zanga yana tuna min lokacin mulkin kama karya’

Atiku Abubakar

Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar ya kirayi jami’an tsaro da su daina harbin masu zanga-zanga kan tsadar rayuwa a faɗin kasar.

Wazirin Adamawa ya yi Allah wadai dangane da rahoton amfani da harsasai da aka samu jami’an tsaro sun yi kan masu zanga-zangar a wasu sassan ƙasar.

Cikin wata sanarwa da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya fitar, ya zargi jami’an tsaron ƙasar da harbin wasu masu zanga-zangar.

Atiku ya ce harbin masu zanga-zangar lumana abin takaici ne, da ya yi kama da na lokacin mulkin kama karya na sojoji.

“Yana da kyau in tuna wa gwamnati da jami’an tsaro game da babban haƙƙinsu na tabbatar da tsaro ga ’yan ƙasar da ke son gudanar da zanga-zangar, wadda ke cikin ’yancinsu da Kundin Tsarin Mulki ya tanadar musu”, in ji Atiku.

A lokacin zanga-zangar an samu rahotonnin harbi a jihohin Kano da Borno da Kaduna da wasu jihohin ƙasar.

Haka kuma, ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta Amnesty, ta ruwaito cewa an kashe aƙalla mutum 13 a ranar farko ta zanga-zangar.

To sai dai Atiku ya ce, a duk lokacin da jami’an tsaro suka buɗe wuta kan masu zanga-zanga, to babu abin da hakan zai haifar illa tayar da yamutsi.

“Ina ƙara jaddada shawarata ga masu zanga-zangar da su jajirce wajen yin amfani da ‘yancinsu ta hayar gudanar da zanga-zangar cikin lumana tare da yin watsi da duk wani lamari da zai tayar da fitina.

“Ina kuma nanata cewa wajibi ne duk waɗanda suke fakewa da zanga-zangar suna wawure kayayyaki da barnata dukiyar jama’a su fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.

“Saboda muddin aka zuba ido kan masu irin waɗannan ayyukan, za su kore halascin zanga-zangar gaba ɗaya.

“Amma fa dole ne Shugaba Tinubu ya nuna jagoranci na gaskiya ta hanyar buɗe ƙofar sauraron koken da jama’a suke yi domin biyan buƙatun al’ummar Nijeriya.”

Atiku wanda a Zaɓen 2023 ya yi takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, ya yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da Kotun Duniya su sanya idanu kan abin da ke faruwa a Nijeriya tare da tuhumar jagororin ƙasar da jami’an tsaro kan abin da suke aikatawa.

HOTUNA: An soma kaɗa ƙuri’a a Zaɓen Ondo

Mai hannu ɗaya da ke sana’ar faskare

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru da kaso 33 a Najeriya — NBS