Harbo jirgin China da muka yi mataki ne da ya dace —Taiwan
Firimiyan kasar Taiwan, Su Tseng-Chang, ya ce matakin kasar na harbo jirgi mara matuki daga gabar tekun iyakar kasar da China abu ne da ya dace.
Firimiyan kasar Taiwan, Su Tseng-Chang, ya ce matakin kasar na harbo jirgi mara matuki daga gabar tekun iyakar kasar da China abu ne da ya dace.
Runudunar sojin kasar ta bada rahoto a ranar Alhamis cewa ta harbo wani jirgi mara matuki da ba na gwamnati ba, wanda ke shawagi a sararin samaniyarta, kusa da wani tsibiri da ke makwabtaka da China.
- Majalisa za ta kara harajin makarantun gaba da sakandare
- Jami’ar Jihar Gombe ta janye daga yajin aikin ASUU
An harbo jirgin ne bayan ya bi ta haramtacciyar hanyar tsibirin inda ya fada teku.
Da yake zantawa da manema labarai ranar Juma’a, Firimiyan ya ce kasar ta sha gargadin yi mata kutse, amma China ta yi kunnen kashi.
“Yin biris da gargadinmu ne ya sa ba yadda muka iya illa mu kare kanmu, saboda shi ne kadai mafita.
“Ba za mu taba tsokanar China ba, amma za mu yi duk mai yiwuwa wajen kare yankinmu da mutanenmu”, in ji shi.
To sai dai China, ta bakin Ministan Harkokin Wajenta ta ce Gwamnatin Taiwan din na kokarin tada zaune tsaye ne kawai.
Kan harbo jirgin dai, kakakin hukumar ya bayyana wa manema labarai cewa kokarin jam`iyar DPP, na zuzuta tashin hankali, ba wani sabon abu ba ne.