Hare-hare: Izala ta nemi Musulmi su dukufa ga alkunuti

Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Ikamatis Sunnah na kasa, Sheikh Abdullahi Bala lau, ya bukaci Musulmin kasar nan su dukufa ga yin addu’o’in alkunuti a masallatai da makarantu da majalisun ilimi na wata daya, don neman taimakon Allah game da tashe-tashen hankulan da aka fama da su a kasar nan.Sheikh Bala Lau yai wannan […]

Hare-hare: Izala ta nemi Musulmi su dukufa ga alkunuti
Hare-hare: Izala ta nemi Musulmi su dukufa ga alkunuti

Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Ikamatis Sunnah na kasa, Sheikh Abdullahi Bala lau, ya bukaci Musulmin kasar nan su dukufa ga yin addu’o’in alkunuti a masallatai da makarantu da majalisun ilimi na wata daya, don neman taimakon Allah game da tashe-tashen hankulan da aka fama da su a kasar nan.
Sheikh Bala Lau yai wannan kira ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofinshinsa da ke Abuja, inda ya ce, “Idan Musulmi suka samu kansu a cikin yanayi marar dadi, to Sunnar Manzon Allah (SAW) ta umarce su da yin addu’o’in da ake kira alkunuti, kuma ita wannan alkunuti ana yin ta ne a lokacin Sallah, idan liman ya dago daga ruku’in raka’ar karshe ta kowace Sallah.”
Ya ce, “Saboda haka mu a wannan kungiya ta Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Ikamatis Sunnah, lura da halin da kasa ta shiga, muka ba da umarni ga dukkan masallatai da makarantunmu da duk majalisi na karantar da darasin Musulunci a ko’ina a kasar nan, cewa ba mu da abin da za mu iya yi kan wannan al’amari face mun koma ga Allah.”
Sheikh Lau ya ce komawa zuwa ga Allah kuwa shi ne, “mu yawaita istigfari da kaskantar da kanmu da zikiri da karatun Alkur’ani da kyawawan ayyuka da nufin Allah Ya taimake mu kamar yadda Yake cewa, ‘Ba don addu’o’in da kuke yi ba, da babu ruwan Allah da ku,” ke nan idan muna son samun taimako daga Allah, to sai mun koma mun kaskantar da kanmu zuwa gare Shi. Don haka muka ba da umarni a yi alkunuti daga nan zuwa wata daya,” inji shi.
Ya ce sakamakon addu’o’in da ake yi abubuwa da dama suna ta bayyana, “Mun yi babban taro a Legas kwanan baya, mun yi addu’a cewa duk wanda ke da hannu cikin kisan gillar da aka yi wa Sheikh Albani Zariya, Allah Ya tona asirinsa, sai ga shi Hukumar SSS sun ce sun kama wadanda suke da hannu a kisansa,” inji shi.
 Sai dai ya ja hankalin jami’an SSS cewa, su bi dukkan abin da doka ta tanada wajen hukunta mutanen, ta hanyar kai su kotu don daukar matakan da suka dace, tare kuma da gano wadanda suka sa su wannan aika-aikar.