Hare-hare: Mun bai wa sojoji umarnin tsaurara tsaro a Zamfara — Matawalle

Ƙaramin ministan ya yaba wa sojoji kan nasarar da suka samu a wasu yankunan Zamfara.

Hare-hare: Mun bai wa sojoji umarnin tsaurara tsaro a Zamfara — Matawalle

Bello Mohammed Matawalle, Ƙaramin Ministan Tsaron Najeriya

Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya umarci sojojin da ke yaƙi da ’yan ta’adda a Arewa maso Yamma da su ƙara ƙaimi tare da ɗaukar matakan gaggawa domin kawo ƙarshen hare-haren da suke aukuwa a Jihar Zamfara.

Umarnin na zuwa ne bayan rahotannin hare-harepan Hukumomi biyu a jihar.

A cikin wata sanarwa da hadiminsa na musamman, Ahmed Dan Wudil, ya fitar a ranar Asabar, Matawalle ya jajanta wa al’ummar Bungudu da sauran yankunan da hare-haren suka shafa.

Ya ce ya umarci jami’an tsaro da su ci gaba da ƙoƙari har sai an ceto mutanen da aka sace tare da murƙushe ’yan ta’addan.

Ministan, ya kuma buƙaci jami’an tsaro su yi amfani da sabbin dabarun yaƙi da kuma tattara bayanan sirri, musamman a lokacin damina, domin samun nasara.

Haka kuma, ya umarci rundunar dakarun Fansan Yamma, wadda ke aiki a jihohin Zamfara, Kebbi, Katsina, Sakkwato da Kaduna, da ta ƙara zage damtse wajen fatattakar ’yan ta’adda.

Matawalle, ya ce dole ne jami’an tsaro su ci gaba da kai samame maboyar ’yan ta’adda tare da ƙara sintiri a wuraren da ake zargin suna amfani da su wajen shirya hare-hare.

Ya kuma yi kira ga shugabannin al’umma da mazauna karkara su riƙa bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai kan masu taimaka wa ’yan ta’adda.

A gefe guda, ya yaba wa jami’an tsaro kan nasarorin da suka samu a yankunan Gummi, Anka, Tsafe da Faskari, tare da ƙarfafa musu gwiwa su ci gaba da yaƙi da matsalar rashin tsaro a Arewa maso Yamma.