Hare-hare na iya hana zaben 2015 a jihohin Adamawa da Borno da Yobe – INEC
Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta yi gargadin cewa ba za ta iya gudanar da zabe a jihohin Adamawa da Borno da Yobe idan aka ci gaba da kai hare-hare a wadannan jihohi.Shugaban Hukumar Farfesa Attahiru Jega ne ya bayyana haka a wurin taron masu ruwa da tsaki na yini dayya da Kwamitin Majalisar Dattawa […]
Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta yi gargadin cewa ba za ta iya gudanar da zabe a jihohin Adamawa da Borno da Yobe idan aka ci gaba da kai hare-hare a wadannan jihohi.
Shugaban Hukumar Farfesa Attahiru Jega ne ya bayyana haka a wurin taron masu ruwa da tsaki na yini dayya da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Zabe da hadin gwiwar Cibiyar Tsara Bayar da Shawarwari kan Harkokin Shari’a da kuma Hukumar Bunkasa kasashe ta Birtaniya suka shirya a Abuja.
Farfesa Jega ya ce: “Hali na dokar ta-baci na nufin ba za ka iya gudanar da zabe na gaskiya da adalci ba. A ka’ida ma ba za ka gudanar da zabe a zamanin da ake gudanar da dokar ta-baci ba. Fatata za a magance matsalolin da ke yankin Arewa maso Gabas kafin shekarar 2015. Idan halin tsaro ya zama ba za mu iya gudanar da zabe ba, za mu koma ga doka mu dakatar da shi ko mu dage shi.”
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ne ya kafa dokar ta-baci a jihohin uku a watan Mayun bana, kuma an kara wa’adinta da wata shida a watan Nuwamba.
Farfesa Jega ya ce Hukumar INEC tana duba yiwuwar gudanar da zaben shekarar 2015 a watan Janairu da Fabrairu, kuma za a bukaci Naira biliyan 93 (kimanin Dala miliyan 514 da rabi) dun gudanar da zabubbukan. Kuma ya yi fatar za su samu kudaden da suke bukata a kan lokaci kafin zaben na 2015.
Ya ce, Najeriya tana da mummunar al’adar siyasa da ke cike da tashin hankali. “Tashin hankali kafin zabe ya jawo mutuwar ’yan siyasa da dama da magoya bayansu da kuma wadanda ba ruwansu. Kuma ana ci gaba da musguna wa masu zabe kuma kungiyoyin ’yan dabar siyasa na ci gaba da watsuwa a tsakanin kabilu a lokacin da ake tunkarar zabe.”
Ya kara da cewa, “A kowane hali zabe a Najeriya harka ce ta wanda ya yi nasara ya kwashe komai, yayin da wanda ya fadi, ke dandana kudarsa kamar na makiyin da aka ci a wurin yaki. Kuma tabbatar da tsaro a zabe shi ne batun da ya fi shafar gudanar da zabe a Najeriya.”
Farfesa Jega ya ce, “Matsalolin rashin zaman lafiya a yanzu suna barazana ga gudanar da zabe. Wadannan sun hada da kai hari ga ma’aikatan zabe ko kayayyakinsu ko kai hari ga jami’an tsaro dfa suke aikin zabe ko amfani da odila-odilan ’yan siyasa ba bisa ka’ida ba da kai hari ga abokan adawar siyasa da kuma kai farmaki ga ma’adanar bayanan intanet na INEC musamman rajistar masu zabe da kuma tashe-tashen hankula a lokacin kamfe.”