Hare-Hare: Rundunar ’Yan sandan Filato ta nemi karin kayan aiki
Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato ta nemi gwamnatin jihar ta samar mata da karin kayan aiki da suka hada da motocin sintiri da babura masu sulke don dakile hare-hare da kashe-kashen da ake yi a tsakar dare a kananan hukumomin Riyom da Barikin Ladi. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Mista Nasiru Oki ne ya bayyana haka […]
Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato ta nemi gwamnatin jihar ta samar mata da karin kayan aiki da suka hada da motocin sintiri da babura masu sulke don dakile hare-hare da kashe-kashen da ake yi a tsakar dare a kananan hukumomin Riyom da Barikin Ladi.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Mista Nasiru Oki ne ya bayyana haka a lokacin da yake yi wa ’yan jarida bayani kan hare-haren da ke ci gaba da faruwa a kananan hukumomin duk da dokar takaita zirga-zirga da aka kafa.
Kwamishinan ya nemi Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya ya kara musu ’yan sanda don kawo karshen hare-haren da kabilar Berom da Fulani suke kai wa juna a jihar.
Idan ba a manta ba mako biyu da suka gabata ne Gwamnan Jihar Simon Bako Lalong ya yi zama da shugabannin kungiyar Miyetti Allah ta Najeriya da Kwamishinan ’Yan sandan don kawo karshen hare-haren da Fulani da Berom ke kai wa juna, sannan ya umarci ’yan sanda su fito da sababbin dabaru da matakan kawo karshen hare-haren.
Sai dai duk da haka hare-haren sun ci gaba da faruwa, al’amarin da ya sanya gwamnatin jihar kafa dokar takaita zirga-zirga a kananan hukumomi daga karfe 6:00 na safe zuwa karfe 6:00 na yamma.
Kwamishinan ya ce duk da karancin jami’ai da suke da shi rundunarsu ta aika da karin ’yan sanda zuwa kananan hukumomin, kuma suna bukatar motocin sintiri da babura masu sulke da karin ’yan sandan don kawo karshen rikicin.
Ya ce “Rikici tsakanin Fulani da Berom ya kwashe shekaru masu yawa, yanzu muna ta fadi-tashin yadda za mu kawo karshensa. Na shaida wa Sufeto-Janar cewa muna bukatar karin ’yan sanda, na kuma yi masa bayanin halin da ake ciki dangane da rikicin.” Ya ce yana da yakinin Sufeto-Janar zai kara musu ’yan sanda don a kawo karshen rikicin.
“A yanzu muna kokarin shirya taron sulhu tsakanin Fulani da Berom don su fahimci babu amfanin su ci gaba da rikici da juna, idan ma ba za su yi sulhu ba, to duk wanda ya ga an kware shi zai iya zuwa kotu, amma ba za mu yarda su ci gaba da kai wa juna hare-hare ba,” inji shi