Hare hare: Sheikh Jingir ya bukaci al’umma su kama azumi da addu’o’i

Shugaban Majalisar Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bukaci al’ummar Najeriya Musulmi da Kirista da marasa addini, su kama addu’o’in rokon Allah Ya kawo karshen hare haren da ake kaiwa a kasar nan. Sheikh Sani Yahya Jingir ya bukaci haka ne a lokacin […]

Hare hare: Sheikh Jingir ya bukaci al’umma su kama azumi da addu’o’i

Sheikh Sani Yahaya JingirShugaban Majalisar Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bukaci al’ummar Najeriya Musulmi da Kirista da marasa addini, su kama addu’o’in rokon Allah Ya kawo karshen hare haren da ake kaiwa a kasar nan.
Sheikh Sani Yahya Jingir ya bukaci haka ne a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a Jos kan harin da aka kai Abuja da sauran hare-haren da ake kaiwa a kasar nan.
Ya ce wannan hari da aka kai Abuja wanda ya jawo asarar rayukan jama’a da sauran hare-haren da ake kaiwa a kasar nan yanzu suna dada nuna cewa tsaro ya karye a kasar.
Sheikh Jingir ya ce tsaron rayukan mutanen kasar nan da dukiyoyinsu yana wuyan gwamnati ne. “Don haka matsalar karyewar tsaron da muke fama da shi a Najeriya laifin gwamnmati ne. Kuma ya zama wajibi masu rike da mukaman gwamnati a kasar nan, su tashi tsaye don ganin an magance wannan matsala,” inji shi.
Ya ce “Kuma ya zama wajibi mu ’yan Najeriya mu yi nadama mu tuba ga Allah kan laifuffukan da muka aikata kuma Musulmi mu rungumi yin azumin ranakun Litinin da Alhamis tare da yin adu’o’i dare da rana. Domin rokon Allah Ya kawo karshen wannan al’amari a kasar nan.”
Ya yi kira ga malaman addini su fito su gaya wa al’umma gaskiya ba tare da tsoro ba, don Allah Ya tausaya Ya kubutar da kasar nan daga cikin wannan hali da take ciki. “Kuma ian kira ga manyan sarakunan kasar nan su tashi su ba da gudunmawarsu wajen ceto kasar nan daga cikin halin da muke ciki. Babu wani sarki da zai ce yana cikin kwanciyar hankali idan al’ummarsa suna cikin tashin hankali. Don haka ya zama wajibi su tashi
su ba da gudunmawarsu wajen ganin an ceto kasar nan daga cikin halin da take ciki,” inji shi.
Ya ce ya wajaba shugabannin kasar nan da sauran al’umma a taru a binciko batagarin da suke yi wa kasar nan makarkashiya domin a yi maganinsu don kasar nan ta zauna lafiya.