Hare-haren bam: Mutum 55 sun mutu a Kano da Yobe

A kalla mutum 37 suka rasu a harin bam da ake zargin ’yan kunar bakin wake da kaiwa a tsohuwar tashar motar Kano Line da Kano a ranar Talata, yayin da 18 suka rasu a makamancin wannan hari da aka kai tashar motar da ake kira Tashar danborno da ake lodin Kano da ke garin […]

Hare-haren bam: Mutum 55 sun mutu a Kano da Yobe
Hare-haren bam: Mutum 55 sun mutu a Kano da Yobe

A kalla mutum 37 suka rasu a harin bam da ake zargin ’yan kunar bakin wake da kaiwa a tsohuwar tashar motar Kano Line da Kano a ranar Talata, yayin da 18 suka rasu a makamancin wannan hari da aka kai tashar motar da ake kira Tashar danborno da ake lodin Kano da ke garin Potiskum a Jihar Yobe.

Hare-haren biyu sun auku ne cikin awa biyu a garuruwan biyu, inda rahotanni suka ce a harin Kano wasu matasa biyu ne suka batar da kama da sunan matafiya suka shiga cikin wata motar kirar Sharon da ke daukar fasinja zuwa Jigawa, kuma shigar su cikin motar ke da wuya sai aka ji fashewar wani abu daga cikinta inda fashewar ta shafi wasu motoci biyu da ke kusa da motar.
Wani ganau ya shaida wa Aminiya cewa ya ga lokacin da matasan suka shigo tashar sai dai babu wanda ya yi musu zargin wani mugun abu, duk da daya daga cikinsu na dauke da jakar matafiya. “Lokacin da matasan suka shigo tashar babu wanda ya kula da abin da suke yi, inda suka nemi mota mai zuwa Jigawa suka shiga, sai dai ba su dau wani lokaci ba muka ji karar fashewar bam inda muka hau gudun tsira,” inji shi.
Wani ma’aikaci a tashar Muhammad Yahaya Umar ya bayyana wa Aminiya cewa mutum18 da ke cikin motar da matasan suka shiga sun mutu, ban da wasu mutanen da abin ya rutsa da su. Wata majiya ta ce ’yan kunar bakin waken sun kone kurmus a lokacin da bam din ya tashi ba kamar yadda ake cewa wai wasu matasa ne suka babbake su har suka mutu ba. Wani jigo a tashar ya ce bincikensu na baya ya gano fasinjoji 21 ne suka rasu, sai ’yan yuniyon uku da masu sayar da kaya 10 da kuma maharani biyu.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ASP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar kamarin inda ya ce mutum 12 ne suka rasu a harin, sai dai bai bayyana yawan wadanda suka jikkata ba.
Aminiya ta kai ziyara Asibitin Murtala inda ta samu bayanin cewa akalla sama da mutum 20 da harin ya rutsa da su suna kwance a asibitin.
A harin Potiskum ana zargin wani dan kunar bakin wake ne ya tada bam a wata tashar kwana biyu kacal da harin bam da wata karamar yarinya ta kai a kasuwar sayar da wayoyin hannu inda mutum shida suka rasu.
Wani fasinja da ya ke gab da wurin lokacin da bam din ya tashi da ya nemi a boye sunansa ya bayyana wa Aminiya cewa, maharin ya zo tashar ne da zimmar zai tafi Kano aka rika mujadala da shi a kan sai an binciki kayansa, kuma ana cikin hakan ne sai bam din ya tashi. Ya ce nan take mutum17 suka rasu yayin da sama da 30 suka ji munanan raunuka.
Har zuwa aiko da wannan labari babu wani jami’in tsaro da ya ce komai dangane da faruwar wadannan hare-hare na Potiskum.