Hare-haren Boko Haram: Gwamnatin Borno za ta sake gina kauyuka biyar
Gwamnatin Jihar Borno za ta kashe Naira miliyan 27 don sake gina wasu kauyuka biyar da ’yan Boko Haram suka kone a karamar Hukumar Jere da ke cikin jihar a harin da suka kai mako biyu da suka gabata.Harin da ’yan bindigar suka kai ya yi sanadin rasuwar mutum takwas a kauyukan da suka hada […]

Gwamnatin Jihar Borno za ta kashe Naira miliyan 27 don sake gina wasu kauyuka biyar da ’yan Boko Haram suka kone a karamar Hukumar Jere da ke cikin jihar a harin da suka kai mako biyu da suka gabata.
Harin da ’yan bindigar suka kai ya yi sanadin rasuwar mutum takwas a kauyukan da suka hada da Wadiya da Kolori da Gambori da Foreri da kuma Koreri a yankin na Jere, kafin su wuce barikin sojojin bataliya ta 21 da ke Giwa a garin Maiduguri.
Da yake jawabi yayin mika kayan masarufin da gwamnatin jihar ta bayar a ziyarar jaje ga mutanen kauyukan, shugaban kwamitin tallafawa da tantance asarar da aka yi na jihar, Dokta Bulama Mali Gubio, ya ce “Gwamnati ta kadu da wannan mummunan hari da ya ci rayukan mutum takwas tare da lalata gidajen mutane da maharan suka yi, inda ya ce gwamnati ba za ta gajiya ba wajen tallafa wa duk wanda bala’in ya shafa. Kuma mun kiyasta yawan asarar da aka yi na kone gidaje da shuguna da kayan masarufi wanda yawan kudinsu ya kai Naira miliyan 27.”
Ya ce idan Gwamnan Jihar Alhaji kasim Shettima ya dawo zai je da kansa don gane wa idonsa irin barnar da aka yi. Ya ce, “Gwamnan ya bayar da umarnin a sake gina gidajenku, to amma a yanzu ga Naira miliyan dai-dai ga kowane kauye tare da kayan abinci da tabarmi da katifu da wasu kayan bukatun yau da kullum.”
Alhaji Gubio ya ce za a bar mutanen kauyukan su ci gaba da zama ba sai an kai su sansanin ’yan gudun hijira ba ganin cewar matasansu suna bakin kokari don kare mutuncinsu.
Da yake karbar kayayyakin a madadin al’ummar kauyen Fori, wakilin Lawanin Fori Alhaji Mustafa Foreri, ya mika godiyarsu ga gwamnatin jihar saboda nuna tausayawa da kawo gudunmawarta a kan lokaci, kuma ya yi alkawarin za a ba duk wadanda abin ya shafa.
Kwamitin ya kai ziyarar ga Bataliya ta 21 da ke barikin Giwa a garin Maiduguri, inda ya jajanta wa sojojin tare da nuna bakin ciki dangane da aukuwar al’amarin, ya kuma mika Naira miliyan daya da kayan abinci da na bukatun yau da kullum ga sojojin.
Shugaban ma’aikata a Bataliya ta 21, Kanar John Ekperere ne ya karbi tallafin a madadin sojojin kuma ya nuna farin ciki da godiya ga gwamnatin jihar saboda irin taimako da hadin kan da take ba jami’an tsaro a kowane lokaci.
A makon shekaranjiya ne ’yan bindigar da ake kyautata zaton ’yan kungiyar Boko Haram ne, suka kai munanan hare – hare a barikin Bataliya ta 21 da ke Giwa a garin Maiduguri da nufin kubutar da ’yan uwansu da ke tsare a barikin bayan sun kai hari a wadancan kauyuka, abin da ya haifar da tsaiko a harkokin kasuwanci da al’amuran yau da kullum a garin Maiduguri, inda aka kakaba dokar hana zirga–zirga ta tsawon sa’o’i 24.