Hare-haren Boko Haram: Matasa sun harzuka a Maiduguri
Sakamamon hare-hare da kwace garuruwa da ’yan Boko Hram ke yi a Jihar Borno da makwabtanta Yobe da Adamawa matasa sun harzuka a garin Maiduguri, inda suka gangamin nuna wa duniya cewa sun shirya domin tunkarar kungiyar Boko Haram a duk lokacin da suka shigo Maiduguri.Matasan wadanda aka fi sani da sibiliyan JTF, sun nemi […]
Sakamamon hare-hare da kwace garuruwa da ’yan Boko Hram ke yi a Jihar Borno da makwabtanta Yobe da Adamawa matasa sun harzuka a garin Maiduguri, inda suka gangamin nuna wa duniya cewa sun shirya domin tunkarar kungiyar Boko Haram a duk lokacin da suka shigo Maiduguri.
Matasan wadanda aka fi sani da sibiliyan JTF, sun nemi a ba su dama da makamai su fuskanci mayakan Boko Haram, sun shaida wa Mai martaba Shehun Borno Alhaji Abubakar Umar Garbai El- Kanemi haka ne a fadarsa makon a farkon wannan mako.
Kakakinsu Barista Jibril Gunda, ya shaidawa wakilinmu cewa, “Muna cikin bakin
ciki kan yadda ’yan Boko Haram ke kashe mutane ba gaira babu dalili da sunan addini, wallahi abin bakin ciki ne kwarai da gaske, domin kuwa wannan abin ba ya da alaka da addini ko kadan, wani abu ne na son zuciya da ra’ayinsu. Don haka ba mu amince ba, kuma ba za mu amince ba, kuma mun bayar da kawunanmu a kan wannan lamari don a samu zaman lafiya a jiha da kasa baki daya, shi ya sa muka kira wannan gangami da ya hada da tsofaffin sojoji da ’yan sanda da jami’an shige-da-fice da kwastam da maharba da mu kanmu.”
Ya ce suna da goyon bayan jami’an tsaro da jama’a kuma sun fito ne domin su gane juna kuma su tabbatar wa mutane suna nan da karfinmu tare da rokon hukumomi su ba su goyon baya ta hanyar ba su makamai don tunkarar ’yan Boko Haram a Bama da Gwoza da dajin Sambisa.
Ya ce sun fi mutum dubu 10, kuma abin da suke so yanzu a ba su makamai za su je su yaki wadancan mutanen don abin ya kawo karshe, “Saboda mun gaji da kashe-kashen da suke yi da jefa mutane cikin wahala musamman yara da mata da suka zama ’yan gudun hijira da ke fama da matsalar abinci da rashin muhalli,” inji shi.