Hare-haren Borno da Yobe sun isa su sanya shugabanni murabus – Da’u Aliyu

Wani mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum Injiniya Magaji Da’u Aliyu ya ce hare-hare da kashe-kashen jama’a da ke faruwa a jihohin Borno da Yobe sun isa su sanya shugabannin hukumomin tsaro na kasar nan su sauka daga mukamansu, kamar yadda hakan ke faruwa a wadansu kasashen duniya.Alhaji Da’u Aliyu ya bayyana haka […]

Hare-haren Borno da Yobe sun isa su sanya shugabanni murabus – Da’u Aliyu
Hare-haren Borno da Yobe sun isa su sanya shugabanni murabus – Da’u Aliyu

Wani mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum Injiniya Magaji Da’u Aliyu ya ce hare-hare da kashe-kashen jama’a da ke faruwa a jihohin Borno da Yobe sun isa su sanya shugabannin hukumomin tsaro na kasar nan su sauka daga mukamansu, kamar yadda hakan ke faruwa a wadansu kasashen duniya.
Alhaji Da’u Aliyu ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Kano, ind ya ce zuwa yanzu ya kamata a ce mahukunta sun dauki matakin da zai kawo karshen hare-hare a kai a kai da ake fuskanta a yankin domin kawo karshen lamarin.
Ya ce “Kamata ya yi a ce Shugaban kasa ya dauki mataki na karshe kuma na ba sani ba sabo, su kuma ’yan majalisarmu kamata ya yi a ce sun zauna sun kawo wani kwakkwaran
kuduri da zai zamo magani na karshe a kan lamarin.”
Injiniya Da’u ya ce abin takaici da ban haushi sai ga shi babu daya daga cikin wadannan abubuwan da mahukuntan suka yi, “Kashe-kashen da aka yi a garuruwan Izge da Bama da na daliban Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Yadin Buni a Jihar Yobe, abu ne da ya isa mahukuntan su sauka su bar mukamansu, kamar yadda hakan kan faru a wasu kasashen duniya,” inji shi.
Ya ce ikirarin da Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima da kuma abin da dattawan jihar suka fada na gazawar jami’an tsaron da aka kai don su samar da tsaro a yankin, ya tabbata gaskiya, tunda kuwa a koyaushe abin sai ci gaba yake yi.
Injiniya Da’u ya kuma nuna goyon baya ga kiran da Sarkin Musulmi ya yi na cewa jama’ar Najeriya su guji tayar da hankali da rikice-rikice a zaben shekarar 2015, amma kuma yana kira ga ’yan kasa su yi aiki da hankalinsu wajen samar wa kansu mafita a zaben mai zuwa. Ya ce, “Wannan shi ne amfanin dimokuradiyya, tsarin dimokuradiyya ya ba jama’a dama idan wata gwamnati ba ta tabuka musu abin kirki ba, kan harkokin rayuwa ko tattalin arziki ko tsaronsu, to suna iya korar wannan gwamnati da kuri’unsu zabi wata domin samun mafita daga halin da suke ciki.”