Hare-Haren Neja-Delta sun jawo wa Najeriya asarar Naira tiriliyan 1.1

Najeriya ta yi asarar Naira tirilyan daya da biliyan 100 na kudin shigar man fetur a cikin wata biyar da suka gabata, sakamakon hare-haren ’yan ta’addan Neja-Delta kan bututun man fetur.Binciken da Aminiya ta gudanar ne ya gano haka, kuma adadin bai hada da asarar da aka tafka a bangaren kudin shigar gas ba, sakamakon […]

Hare-Haren Neja-Delta sun jawo wa Najeriya asarar Naira tiriliyan 1.1
Hare-Haren Neja-Delta sun jawo wa Najeriya asarar Naira tiriliyan 1.1

Najeriya ta yi asarar Naira tirilyan daya da biliyan 100 na kudin shigar man fetur a cikin wata biyar da suka gabata, sakamakon hare-haren ’yan ta’addan Neja-Delta kan bututun man fetur.
Binciken da Aminiya ta gudanar ne ya gano haka, kuma adadin bai hada da asarar da aka tafka a bangaren kudin shigar gas ba, sakamakon fasa bututun da suke kai gas da kamfanonin samar da wutar lantarki na cikin gida da masana’antu da kuma wanda ake fitar da shi.
Binciken ya gano kungiyar mayakan Niger Delta Abengers (NDA) sun kai hare-hare 28 kan bututun mai daga ranar 10 ga Fabrairu zuwa karshen watan Yulin bana.
kungiyar ’yan ta’addan ta ayyana tsagaita wuta a daidai lokacin da sojojin Najeriya suka kaddamar da wani shiri mai suna Operation Crocodile Smile, wanda manufarsa kawar da ayyukan ta’addanci a yankin mai arzikin mai.
Ana asarar tiriliyoyin Naira
Kasafin kudin bana ya ginu ne a kan za a rika hako man fetur ganga miliyan biyu da dubu 200 a kullum, sai dai hare-haren sun sa abin da ake hakowa ya yi kasa da kimanin kashi daya cikin uku na abin da aka kiyasta daga watan Afrilu zuwa 29 ga Agustan bana.
Alkaluman da Kamfanin Man Fetur na kasa (NNPC) ya fitar sun nuna an samu koma baya wajen hako man da ganga dubu 300  a watan Afrilu. Kuma a watan Mayu, Minista a Ma’aikatar Man Fetur, Dokta Ibe Kachikwu ya ce man da ake hakowa ya sake komawa baya da ganga dubu 600, inda aka hako ganga miliyan daya da rabi a kullum.
Sannan a watan Yuni da Yuli ya sake komawa baya inda ake asarar hako ganga dubu 700 a kullum, sai kuma a ranar Alhamis din makon jiya ya sake yin kasa da ganga dubu 800, inda ake iya hako ganga miliyan daya da dubu 400.
A bisa farashin mai na Dala 42 da digo 02 da Dala 46 da digo 94 kan kowace ganga, kuma a bisa musayar Dala a kan Naira 197 a watan Afrilu da Mayu, Najeriya ta yi asarar kudin shiga da ya kai Dala miliyan 378 wato Naira biliyan 75 da Naira biliyan 171 a jere.
Bayanan Babban Bankin Najeriya (CBN) da Kamfanin NNPC,  sun nuna an rika sayar da gangar man a watan Yuni da Yuli a kan Dala 48 da digo 79 da Dala 41 da digo 37, yayin da darajar Naira take tsakanin Naira 285 da 292 kan kowace Dala daya. Don haka mayakan NDA sun jawo wa Najeriya kudin shiga na man fetur da suka kai Naira biliyan 292 da biliyan 262 a watannin biyu.
Sannan yayin da ake sayar da gangar mai a kan Dala 48 da digo 31 kuma ake canja Dala a kan Naira 305, an kiyasta cewa Najeriya ta yi asarar kudin shigar mai na kimanin Dala 112 ko Naira biliyan 341 a kwanaki 29 na watan Agusta.
Jimillar kudin shigar man fetur (ban da gas) da aka yi asara a tsakanin watan Afrilu zuwa 29 ga Agusta ya kai Naira tiriliyan 1 da biliyan 140.
Kuma hare-haren na kungiyar NDA ya jawo Najeriya tana fitar da man fetur mafi karanci a cikin shekara 30 da suka gabata, inda hakan ke barazanar jawo asarar kudin shigar da za a samu daga man fetur a kasafin bana da fiye da Naira biliyan 820.
Manyan kamfanonin mai sun dakatar da aiki
A cikin watanni biyar da suka gabata, an samu gagarumar tarnaki wajen fitar da man fetur daga kasar nan, saboda kamfanonin man fetur mafiya girma hudu daga cikin biyar masu fitar da mai sun dakatar da aikinsu kwata-kwata.
Yanzu haka manyan wuraren haka da fitar da mai na Forcados da kua Iboe da Bonny Light da Kogin Brass suna aiki ne da wata doka da ake kira dokar fuskantar muguwar barazana, wanda a karkashinta hakan ya ba kamfanonin damar dakatarwa ko jinkirin kai kaya saboda tsoron abin da ka iya biyo baya.
Kamfanin Shell na Najeriya ya riga ya ayyana dokar saboda ya ce yana fuskantar mugun kalubale game da dakon mai daga tashar fitar da mai ta Forcados tun ranar 21 ga Fabrairun bana, bayan da ’yan ta’addan suka tayar da bam a bututun da yake kai mai tashar ta Forcados, lamarin da ya jawo asarar ganga dubu 250 na danyen mai a kowace rana.
Wani babban kamfanin mai ma a ranar 12 ga Agusta ya ayyana aiki da dokar wajen fitar da mai daga tashar Bonny Light sakamakon rufe mashigin ruwa na Nembe Creek Trunk Line (NCTL)  da masu kula da bututun yankin wato Aiteo, ya yi saboda yoyon da yake yi. Ayyanawar ta zo ne bayan wata da janye aiki da dokar fuskantar mugun yanayi da ya ayyana kan hanyar a ranar 10 ga Mayu.
Sai dai tashar fita da mai ta Bonny Light tana ci gaba da aiki tabututun  Trans Niger Pipeline, wanda aka sake budewa bayan ya kasance a rufe tun farkon watan Yuni.
Shi ma kamfanin EddonMobil ya ayyana aiki da waccan doka kan fitar da mai ta jiragen ruwa daga kua Iboe bayan aikin hakar ya samu matsala kuma bututun da suka mallaka tare da Kamfanin NNPC ya lalace.
kua Iboe shi ne magangara ko rijiyar mai ta Najeriya mafi girma da ake fitar da mai, inda galibi ake haka da fitar da ganga dubu 300 a kullum. Kuma a bara tasharta tana iya samar da ganga dubu 342 na danyen mai a kullum.
Yanzu dai ba a sani ba ko kamfanin mai na Eddon Mobil zai iya amfani da kananan bututu a matsayin wani zabi na dawo da fitar da mai ta hanyar kua Iboe. Babu wani tsari da ya bayyana na yin gyara a kai. Sannan ana jan  kafa kan tsarin da aka yi wa Erha da Bonga kamar yadda kamfanin Dillancin Labarai na Rueters ya labarto.
A watan Afrilu,  wani babban kamfanin mai na kasar Italiya mai suna Eni ma ya ayyana aiki da dokar fuskantar barazana a rijiyarsa ta Kogin Brass, bayan tashin gobara a wani bututun mai. An dage dakatarwar bayan kwanakin kadan. Sai dai kasa da wata daya kamfanin ya sake ayyana dokar sakamakon harin da aka kai wa wani babban bututu da ke gabar Kogin Brass.
Hare-haren na barazana ga kasafin bana
Da yake bayani kan illar da ci gaba da kai hare-haren ke yi ga tattalin arziki, Dokta Kachikwu ya fadi a ranar Alhamis din makon jiya cewa, baya ga matsalar faduwar farashin man, Gwamnatin Tarayya ta yi asarar kashin 50 cikin 100 na kudin shigarta, haka ma jihohi da kananan hukumomi.
“Ayyukan ’yan ta’addan sun kawo koma baya ga hako mai daga gangan miliyan 2 da dubu 200 a kullum zuwa kusan ganga miliyan 1 da dubu 400.  Idan aka lura da abin da nake cewa a nan, muna kokarin komawa ga hako ganga miliyan 1 da dubu 300 ke nan. Hakan yana nufin idan aka hada faduwar farashin mai da adadin wanda ake hakowa an samu asarar fiye da kashi 60 cikin 100 na kudin shigar kasar nan ke nan,” inji Kachikwu.
Ya kara da cewa: “Ke nan ba za ka iya samar da kudin kasafin bana. Idan kuma ba za a samu kudin kasafin ba, gwamnati ba za ta samu kudi ba ke nan, ba za a biya albashi ba, ba za a gudanar da gine-ginen gwamnati ba, babu wani ci gaba da zai samu.”
Minsitan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare Udoma Udo Udoma a kwanakin baya ya ce Najeriya ta yi asarar kudin shiga da ya kai Naira tiriliyan daya da biliyan 64 a cikin wata shida na farkon bana, wato kasar nan ta yi asarar kashi 55 na kudin shigar da take sa ran samu.  
Jihohi na tsaka mai wuya
Jihohi ma na dandana kudarsu sakamakon faduwar kudin shigar man fetur. Lamarin ya yi kamari ta yadda wasu jihohi suka koma gida babu ko kwabo a watan Afrilun bana, bayan an cire basussukan da ake bin su daga kason Tarayya.
Kimanin Naira biliyan 32 aka cire daga kason jihohin a lokacin rabon kason tarayya na watan Afrilun saboda nau’o’in basussukan da suke kansu.
Misali Jihar Osun kasonta na Naira biliyan biyu da miliyan 30 na watan ya tafi wajen cire bashin da ake bin ta na Naira biliyan biyu da miliyan 391, lamarin da ya nuna ta koma gida da bashin Naira miliyan 361 a kanta.
Hatta jihohi masu arzikin mai ba su sha daga wannan hali ba, inda Jihar Bayelsa  ta rasa Naira biliyan uku da miliyan 207 daga cikin kasonta na Naira biliyan hudu da miliyan 812 ga biyan bashi a watan na Afrilu.
kididdigar hukuma ta nuna jihohi takwas masu arzikin man fetur da suka hada da jihohin Bayelsa da Ribas da Delta da Akwa Ibom da Edo da Imo da Ondo da kuma Abiya sun raba Naira biliyan 20 a matsayin kashi 13 cikin 100 na man da ake hakowa daga jihohinsu a watan Yuli.  Wannan adadi bai kai kashi 10 cikin 100 na kudin man da suke samu ba, kafin shiga wannan hali na faduwar darajar mai da hare-haren ’yan ta’addan ba.
Sakamakon haka galibin jihohin da suke yankin Neja-Delta suna fuskantar tagwayen kalubale na biyan albashi da kuma aiwatar da ayyukan raya kasa.
Bayanin kwararru
“Baya ga koma bayan tattalin arziki, muna kuma rasa yawan mai da gas da ake hakowa, farashin ba ya da armashi, don haka abin ya zama daurin gwarmai ga kasar nan,” Akinyemi Akingbade, wani kwararre kan harkan fetur da gas da ke Legas. Ya kara da cewa: “Idan gwamnati ta tsara hakowa da fitar da ganga miliyan 2.2 a kullum, amma ta dawo tana iya fitar da ganga miliyan 1.6 sannan farashi ya fadi, wannan babban abin bakin ciki ne ga kasa.”
Shi kuwa Shugaban Nazarin Makamashi na Rukunin Bankunan Ecobank, Mista Dolapo Oni cewa ya yi, illar da hare-haren suke yi wa tattalin arziki a yankin yana bayyana ta hanyoyi biyu. Ya ce adadin man da ake hakowa na rage kudin shigar mai yawa da gwamnati ke sa ran samu. “Sannan dan kadan din da aka samu ana kashe su wajen gyara bututun man da aka lalata,” inji Oni.
Kakakin kungiyar Manyan Ma’aikatan Fetur da Gas na Najeriya (PENGASSAN), Mista  Emmanuel Ojugbana ya ce duk da cewa babu hadarin rasa aiki, amma tsaron rayuka da lafiyar ma’aikatan man a yankin babban abin damuwa ne. Ojugbana ya ce yana jin tsoro idan aka ci gaba da kai hare-haren ma’aikata a bangaren suna iya rasa ayyukansu.