Hare-haren Ukraine ba sa nasara a kan Rasha — Putin
Ukraine a hare-haren martanin ta ce ta samu galaba a gabashin Donetsk.
Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha ya ce hare-haren martani da kasar Ukraine ke kaiwa ba sa yin nasara, hasali ma sojojin Ukraine na asara sosai.
Da yake magana a wani taron manema labarai na da ke aika rahotanni kan yaki, ya ce asarar da Ukraine ke tafkawa ta kama hanyar kaiwa wani mummunan mataki.
- Yadda wasu ‘kamfanonin waje’ ke koya wa matasan Najeriya damfara
- Shirin gasar fitar da zakarun jima’i a Sweden ya tarwatse
To sai dai babu wanda ya tabbatar da wannan ikirari na Mista Putin, kuma Shugaba Zelensky na Ukraine ya musanta cewa ba sa samun nasara.
A yayin taron manema labaran Shugaban Putin wanda ya yi ikirarin cewa Ukraine ba ta samun nasara a martanin da take kaiwa a yakin da kasarsa ke yi da ita, ya furta kalaman ne kawai ba tare da gabatar da wata shaida ba, inda ya ce Ukraine ta yi asarar manyan motocin yaki na igwa sama da 160, yayin da kasarsa ya ce guda 54 kawai ta rasa.
Kuma ya ce asarar dakarun Ukraine ke yi ta ninka wadda Rasha ta yi sau goma, yana mai kafewa da nanata cewa ba wani bangare da Kyiv ta yi nasara a yakin.
Sai dai wani jami’in Amurka da ya nemi a sakaya sunansa ya gaya wa Kamfanin Dillancin Labarai na AP cewa, bayanan Putin ba daidai suke ba, ya kuma ce kada a dauki kalaman na Moscow da muhimmanci.
Haka Shugaba Zelensky na Ukraine wanda ya yi watsi da kalaman na Mista Putin a jawabin da ya saba gabatarwa ta bidiyo da daddare, ya ce martanin nasu na samun nasara, inda ya mika godiya ga dakarun kasarsa kan duk wani taki na kasar da ya ce sun kwato daga masu mamayar tasu.
Babban Kwamandan Sojin Ukraine Valery Zaluzhny, ya nanata kalaman Shugaba Zelensky inda ya rubuta a shafinsa na sada zumunta da muhawara na Telegram cewa suna ganin tasiri da nasara a hare-haren kuma ya ce suna aiwatar da tsare-tsarensu kamar yadda suke, inda suke yin gaba-gaba.
Ukraine a hare-haren martanin ta ce ta samu galaba a gabashin Donetsk.
Haka kuma Shugaba Zelensky ya ce suna samun nasara inda suke matsawa a Bakhmut.
Sai dai yanayin ba a fayyace yake ba kamar yadda Ukraine ke ikirarin nasarar da ta bayyana a farkon makon nan.
A ranar Talata sojin Ukraine sun bai wa BBC damar shiga wasu daga cikin yankunan gabashin Donetsk da suka kwato aka kuma kafa tutar Ukraine.
Yankuna da dama ba kowa kuma akwai alamun dakarun Rasha sun ja baya.
Shugaban Kungiyar Tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg, ya ce duk da cewa zai zama wani hanzari a ce an yi galaba a kan Rasha, to amma a bayyane take cewa an kora sojojin mamayen baya.