Hare-haren ’yan bindiga sun tsananta bayan sace Janar Rabe — Al’umma

Maharan sun riƙa bi gida-gida suna yi wa mutane barazana, tare da yi wa wasu bulala da kuma kwashe kayan abinci da dabbobi.

Hare-haren ’yan bindiga sun tsananta bayan sace Janar Rabe — Al’umma

Al’ummomi a ƙananan hukumomin Kankia da Musawa da Matazu a Jihar Katsina sun ce hare-haren ’yan bindiga sun sake ƙaruwa tun bayan sace Manjo-Janar Rabe Abubakar da matarsa.

Lamarin da ya sake jefa al’ummomin karkara cikin fargaba, a yayin da mazauna yankin da dama ke danganta taɓarɓarewar tsaro da janye sojoji daga wasu sassan yankunan da abin ya shafa.

Mazauna sun bayyana cewa janyewar sojojin ya sake barin al’ummomin cikin haɗarin hare-haren ’yan bindiga.

Sun shaida wa wakilinmu cewa, wasu ’yan bindiga masu biyayya ga fitaccen shugaban ’yan bindiga Kachallah Muhammad sun kai hare-hare a wasu ƙauyuka, ciki har da wata rugar Fulani da ke kusa da garin Matazu, inda suka kashe mutum biyu.

Sun ce harin ya kawo ƙarshen ɗan kwanciyar hankalin da aka samu bayan tura jami’an tsaro zuwa yankin sakamakon sace Janar Rabe.

“Muna jin daɗin ɗan kwanciyar hankalin da aka samu ne sai ’yan bindigar suka sake kawo hari. Sun zo da yawa, suna ta harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa. Mutum biyu suka mutu nan take, sauran mutane kuma suka rika tserewa domin tsira da rayukansu,” wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu.

Mazauna yankin sun ce maharan sun riƙa bi gida-gida suna yi wa mutane barazana, tare da yi wa wasu bulala da kuma kwashe kayan abinci da dabbobi.

“Sun wulaƙanta mu tamkar ba mu da wata daraja. Sun gaya mana cewa babu wanda zai sake kare mu. Wannan magana kaɗai ta jefa al’ummarmu cikin matsananciyar fargaba,” in ji wani mazaunin yankin.

 

Manoma sun shiga tsaka mai wuya a Kankia

Sun kuma ce hare-haren sun bazu zuwa Ƙaramar Hukumar Kankia, inda ake zargin ’yan bindigar sun kai hari kan manoman da ke shirin noma da injuna.

Rahotanni sun nuna cewa maharan na neman man fetur ne domin amfani da shi a babura, bayan da Gwamnatin Jihar Katsina ta haramta sayar da fetur a cikin jarkoki.

Manoma sun ce duk da cewa matakin na da nufin hana ’yan bindiga samun fetur cikin sauƙi, ya kuma jefa mazauna karkara cikin matsala saboda dogaron da suke yi da injunan noma masu amfani da fetur.

“Zuwa sayen fetur yanzu ya zama tafiyar da babu tabbacin dawowa. Kana iya haɗuwa da ’yan bindiga a hanya, amma ba za ka iya noma ba tare da fetur ba saboda da yawa daga cikinmu yanzu muna amfani da injuna,” in ji wani manomi a Kankia.

Wani manomin kuma ya nuna rashin jin daɗinsa kan abin da ya bayyana a matsayin saurin janye sojoji kafin lokacin da ya dace.

“Mun yi zaton aikin zai ci gaba har sai an kawar da dukkan maɓoyar ’yan ta’adda da masu ba su haɗin kai. Amma yanzu da alama sojojin sun tafi, kuma tsoro da kashe-kashe da garkuwa da mutane da ta’addanci sun sake dawowa,” in ji shi.