Hargitsin sakatariyar PDP ya hana taron unguwanni a Jihar Oyo
Taron unguwanni (ward congress) da jam’iyyar PDP ta gudanar a jihohin kasar nan baki daya a ranar Asabar da ta wuce, ya samu cikas a Jihar Oyo saboda barkewar hargitsi da safiyar ranar Asabar, inda wasu ‘yan bangar siyasa da suka tarwatsa mutane da lalata wasu muhimman kayan zabe da suka yi awon gaba da […]
Taron unguwanni (ward congress) da jam’iyyar PDP ta gudanar a jihohin kasar nan baki daya a ranar Asabar da ta wuce, ya samu cikas a Jihar Oyo saboda barkewar hargitsi da safiyar ranar Asabar, inda wasu ‘yan bangar siyasa da suka tarwatsa mutane da lalata wasu muhimman kayan zabe da suka yi awon gaba da wasu muhimman takardu da aka tanada a sakatariyar PDP a Ibadan. Ana kyautata zaton wadannan ‘yan banga suna daga cikin magoya bayan wani mai sha’awar tsayawa takarar kujerar gwamna a karkashin inuwar PDP a zabe mai zuwa ne a Jihar Oyo, hart a kai ga an kasa gudanar da wannan taro.
’Yan sandan kwantar da tarzoma da aka girke a sakatariyar jam’iyyar PDP su ne suka taimaka wajen shawo kan matsalar kafin ta kazance. Wasu bayanai da ba a tabbatar ba, daga sassa daban-daban na kananan hukumomi 33 na Jihar Oyo, sun nuna cewa, an gudanar da wannan taron ne a wasu wurare ba tare da yin taron a sauran unguwanni ba.
Hedkwatar jam’iyar PDP daga Abuja ta nada wani kwamiti da zai binciki dalilin da ya hana yin taron na unguwanni a Jihar Oyo a wannan rana. Kwamitin da ke karkashin shugabancin Farfesa Alphonsus Nwosu, ya fara zama ne a ranar Litinin a Sakatariyar jam’iyyar, inda ya saurari korafe-korafen da wasu masu son tsayawa takarar kujerar gwamna suka gabatar masa.
Wasu da ke son tsayawa takarar mukamin gwamna a karkashin inuwar jam’iyar PDP a Jihar Oyo, da suka hada da tsohon ministan wasanni Farfesa Taoheed Adedoja da Sanata Ayo Adeseun da Mista Femi Babalola da Mista Seyi Makinde da Kehinde Olaosebikan da Farfesa Soji Adejumo, su kadai aka gani a wajen zaman kwamitin. Shi kuwa tsohon Gwamnan Jihar, Christopher Adebayo Alao Akala da tsohon jagoran wakilan majalisar dattijai Sanata Teslim Folarin da tsohon minister, Wole Oyelese ba su halarci zaman kwamitin ba, kuma ba su aika da wakilansu ba.
Shi ma Dokta Isaak Owolabi, bai halarci zaman kwamitin ba, amma ya aika da wakilinsa tare da zargin shugabannin jam’iyyar na Jiha da ci gaba da yin wannan taro, domin fito da sakamakon da suke so. Ya nuna bakin cikinsa ga matakin ci gaba da yin taron na unguwanni, duk kuwa da irin hargitsin da ‘yan banga suka tayar a sakatariyar jam’iyyar da wuraren taro masu yawa.
“Ba a yi taro a unguwar da na fito ba wato, ward 1, a karamar Hukumar Ibadan ta Gabas, domin ’yan banga ne suka mamaye wannan wuri,” inji shi.
Daga cikin korafe-korafen da kwamitin ya fara saurara ta bakin wasu masu son tsayawa takarar, sun hada da rashin gudanar da taron a unguwannin sassa daban-daban na jihar da layar zana da kayayyakin aiki suka yi a sakatariyar jam’iyyar da ke Ibadan. Sai dai kuma, wasu daga cikin su sun ce an yi taron da zaben shugabanni ne ba tare da muhimman kayan aiki ba.
Da yake amsa tambayoyin ’yan jarida kakakin jam’iyar PDP a Jihar Oyo Hon. Kehinde Salawu, ya ce, sun ci gaba da gudanar da taron ne a unguwannin jihar baki daya ne saboda akwai kwafe na irin takardun da aka lalata a tare da jam’iyyar.
“Amma jami’an hukumar zabe (INEC) da suka halarci wannan wuri domin gudanar da taron su ne kadai za su bayyana gaskiyar abun da ya auku,” inji shi.