Hari a cibiyar Ebola a Laberiya ya jefa jama’a cikin dar-dar
Gwamnatin Laberiya ta ce ta gano dukkan mutum 17 da aka ce suna dauke da cutar Ebola amma suka kubuce bayan hari da aka kai wata cibiya da aka killace su a karshen mako.Ministan Labaran kasar, Lewis Brown ya fada wa BBC cewa an kai mutanen zuwa wata cibiyar lafiya ta kwararru.An tsaurara tsaro a […]
Gwamnatin Laberiya ta ce ta gano dukkan mutum 17 da aka ce suna dauke da cutar Ebola amma suka kubuce bayan hari da aka kai wata cibiya da aka killace su a karshen mako.
Ministan Labaran kasar, Lewis Brown ya fada wa BBC cewa an kai mutanen zuwa wata cibiyar lafiya ta kwararru.
An tsaurara tsaro a cibiyoyin killace masu Ebola bayan akai wa cibiyar hari lamarin da ya sanya jama’ar kasar zaman dar-dar cewa cutar na iya ci gaba da yaduwa a kasar.
Alkaluman Hukumar Lafiya ta Duniya na baya-bayan nan sun ce kimanin mutum 1,229 ne zuwa yanzu suka mutu sakamakon cutar Ebola, kuma mafi yawancinsu daga Laberiya suke.
Lewis Brown ya ce an kai harin ne a cibiyar da ke West Point wanda ya so kawo koma-baya ga yaki da cutar a Liberiya.
Wasu mutane ne suka farma wani wuri da aka kebe mutanen da suka nuna alamun cutar Ebola inda suka sace kayan mutanen da aka kebe, ciki har da zannuwan gado da katifun masu jinyar.
Wakilin BBC a Manrobiya ya ce: “Mutanen unguwar na nuna damuwar cewa saboda wasu daga cikin katifun da shinfidun da aka sace na da jini-jini da amai a jikinsu, to cutar za ta iya yaduwa a unguwar wadda dama can mutanenta na fama da talauci.”
Rohotanni sun ce mutanen da suka kai hari kan sansanin Ebolan na nuna takaicinsu ne saboda kafa cibiyar a unguwarsu ba tare da tuntubarsu ba.