Harigidon hargowar harshe (3)

Masu yaren Hau-hau wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa ba na shan hantara da harara, har ma da kyara daga ’ya’yan yanyawar da aka yi wa harsunansu Barbara. Lamarin  kuwa ya auku ne saboda kusan  kowa na yin batu a cikin harshen da aka fi ji a daukacin Yammacin Ifrikiya. kasurar yaren Hauhau wajen […]

Harigidon hargowar harshe (3)

Masu yaren Hau-hau wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa ba na shan hantara da harara, har ma da kyara daga ’ya’yan yanyawar da aka yi wa harsunansu Barbara. Lamarin  kuwa ya auku ne saboda kusan  kowa na yin batu a cikin harshen da aka fi ji a daukacin Yammacin Ifrikiya. kasurar yaren Hauhau wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa ba, ta kai a ce an fara horar da dalibai koyon watsattsake da buda wagagen littafai a fannonin ilim in da ya kamata a ce an baje su a faifai. kin aiwatar da wannan tsari ya haifar wa kwakwalen al’umma zama kufai.

Da ana horar da ’yan dugwi-dugwi kimiyyar sarrafa sinadarai da kimiyyar nazarin halittu da injiniyanci da Binciken Bokan Turanci da alkiblar faskaren wasikun  jakin-dawa da na gida, tuni da takunmu ya hau turbar yin kafada-da-kafada da ci gaban kasashen duniya, musamman a Turai da Asiya. Kai da uwargida ta dade da kwarewa wajen dabarun sarrafa ungurnu da manda da kanunfari da citta da tafarnuwa da sauran  kayan yaji, masu maganin mura da kyautata dandanon baki ga cusa annashuwa da kuzari. Ga cinda zugu ko bi-ni-da-zugu da aka ce wai masana sun lalaubo dabarun sarrafa shi ya bayar da makamashi kamar man TUNKUZA da ke bai wa mahaya  ababen hawa dama su TAGAZA ka da su GAZA. Ina masu hakar KUZA  sai a MAZAYA, a MAZAYA a yi ta aikin GAYYA da kwazon matuka GAYA. Wannan babu JAYAYYA!

Haurobiyawa ya zame mini dolen-dole in bijiro da wannan batu na kasurar yaren hau-hau wajen  hawan sa ba tare da sa-in-sa ba, jin cewa ana ta hatsaniyar da hargowar harsuna a kasar Haurobiya wai saboda Baban-burin-huriyya ya aiko da gaisuwar sallah, amma bai ba mu salala ba, ballantana mu kara kuzari ka da mu yi kasala. Duk da haka wasu ’yan ba ni na iya sun yi matukar kokawa kan yadda aka yi ya isar da sakon gaisuwarsa ga al’ummar kasa cikin HARSHEN GIDA da aka gada, alhali a hukumance murguda baki ake yi kamar ana cin kilishi, a kan ga gilashi a yi ta yaren Ingilishi, wato dai WHY COULDN’T HE TSUGILAGI TURANCI AND SOMETIMES kOBOBO? Kodayake ni ba ni da masaniya game da hujjar Baba ta kalallame kalamai a cikin yaren Hau-hau wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa ba, amma dai nasan cewa har Turawan Turai da Larabawan Larai suna da masaniyar cewa duk harshen da ke jinko bakin al’amura ya yi cushe a cikinsa zai ci gaba da rayuwa fiye da yadda ake zato. Watakila ma wannan shi ne dalilin da ya sanya Turawan Turai suka kafa sashen  Hawan-sa a akwatin magana na Babbban Bakin Ce-Ce-Ku-ce na Birnin Lantsandan; an yi kurmusun kalmomi a kAMUSUN JAMUS, musamman a akwatin magana na DUT-KU-CALLE DA WALLE-WALLE KA DA KU KACACCALE, tunda an hana tashen MACUKULE, har wasu su fara kalle-kalle, ballantana a sake lale, kafin a saka amarya a lalle; shi kuwa Babban mutum mai rawani ya dare bisa amale, maimakon a kada masa tambari sai a yi ta dukan talle. Kai Muryar Amurkawa ma tana da sashen shirye-shiryenta a cikin yaren Hau-hau wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa ba. Kuma tuni Ifrikiyya ta zamto SANSANIN SINAWA don haka bata lokaci ne ma a ce ko mutanen kasar Sinu suna sane ko sun iya furta kalamai a cikin harshen harasunan Ifrikiyya?

BOBO DA kWAkMBON BOKOKO wajen laluben na koko, musamman mu da muke Haurubja bangaren Utako a garin tako-tako cikin dakin katako, lallai kada mu yi sako-sako har larurar laulayi ta lula da mai LAMBO. Kai ni ina ganin ma gara mu dukuga wajen zayyana SALO-SALO, musamman a karatubn ALLO.

’Yan makaranta zan karkare batutuwana da yi muku matashiya kan yadda aka sha bamban wajen faskaren ma’anonin kalaman Baban-burin huriyya. Domin na tuna lokacin da ya taba furta cewa a fafutikar WASAN SAMSON-SIYA-SIYA DA kWAkWALEN TALAKAWA WAJEN KAFUWAR DAMO-DA-KURA-DA-dIYYA cewa za a yi “KOLO JINI, BIRI JINI,’ wato daf da kada kuri’un zabi-sonka na shekara ta dubu karamin lauje da sili da babban lauje. Babu wanda ya duba kurmusun kamusun Haurobiyawa, musamman na yaren Hau-hau wajen hawansa ba tare da sa-in-sa ba, ballantana a samu saukin faskara ma’anoni yadda ya kamata. Haka aka yi ta shaci-fadi da suka-da-burtsatsen maganganu, inda wasu suka karke da shan kunu.

Uwa-uba a karo na karamin lauje wasu da ba su fasko korafin uwargidan Baban-burin-huriyya ba, sai suka baza wa duniya cewa ta shiga Babban Bakin Ce-ce-Ku-ce na birnin Lantsandan ta caccaki gwamnatinsa. Shi kuwa gogan naku da ya tabbatar an ki fasko lamarin da gangan, sai ya furta cewa uwargidansa tana da kimar mutuntaka da matsayi a dAKIN GIRKA KAYAN dUNdUME kURURU da GUDAR TURAKAR. Ganin cewa ya furta wadannan kalamai a gaban Uwargida Anjela Mai-makin rikon ragamar Jamusawa, nan ma sai aka yi ta baza bezar Buzuzun zuzuta al’amuran kanzon kurege. daukacin al’umma ba su da masaniyar cewa akwai uwargidan Farin-minista a kasar Japan, wato Akie Abe da ke adawa da gwamnatin maigidanta, har ma zuwa take wajen baje kolin yadda ake girka kayan dundume kururu na kasar Koriya ta Kudu, wadda ke takun saka da kasarta; kuma tana gabatar da shiri na musamman a akwatin magana mai hoto.

Sannan a matsayina na Baban Direban Allin wannan farfajiya ta Dodorido da ke cikin Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya, lokacin aikin hajjin bara Balarabe ya bijiro mini da tambaya cikin yaren Hau-hau wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa ba, wato wai ‘MATANKA NAWA? Cikakken bayani dai na cikin makalar makaranta mai taken AIWA DA KOYIS.

Turawan Turai da Larabawan tsakiyar gabashi sun kasura ne ta hanyar kalallame kalamai da manufa takamaimai a cikin harsunan gida da aka gada iyaye da kakanni, har ma ’yan mata na yi musu gada da wakar barar gyada, inda sukan gyada kai da rangwada. Sannan faskaren ma’anonin litattafan addini da na kimiyya da sauran fannonin rayuwa sun yi matukar tasiri wajen tumbatsa da yaduwar kowane irin harshe a fadin duniya. Biusa wanan dalili uya zama wajibi mu yi KISHI harsunanmu, mu daina yi musu kisan mummuke saboda mun iya kan ga GILASHI, muna murguda baki, tamfar masu cin KILISHI, wai mu ga gwanayen INGILISHI.

Kuma ina mai tabbatar muku cewa, da zarar mun daina HARIGIDON HARGOWAR HARSHEN HAUROBIYA, Turawa ma za su yaba mana, har ta kai ga an ce a fannin watsattsake da buda wagagen littattafai Malam Bubakari dan Imami ya zama Limami wajen samar da JARIN MAGANGANUN MAGANCE MATSALOLIN MUTANE. Shi ke nan BALA DA BABIYA sun bude mana sabon babin inganta UWAR JIKI; dANDUNA DA WAKALE A ZANGON GYARA, sai mu yi ta tsuwurwurta managartan gyare-gyare, amma ba ‘’YAN GYARE-GYARE IRIN NA GYARE DA KUREGE ba.

Haurobiyawa akwai bukatar kusan kima da darajar harsunanku, ta yadda idan aka cusa su cikin manhaja mara hajijiya, likitocinku da injiniyoyinku da malamanku da daukacin masu watsassake a shafukan mujallu da makalu za su rika cin jarrabawa da gwagwaban maki. Sai mu yunkura wajen fatattakar HARGOWAR HARSUNAN HAUROBIYA. Kowa na da damar yin kURMUSUN kAMUSUN JAMUS da askin KWAS-KWAS, musamman ma saboda KWAS din  CIN CA’AMMAS abincin gayun TAGADAS BABU MAGWAS, har ma ana iya karawa da cin KUSKUS ko a ji dadin yin kUSkUS!