Sojojinmu sun kashe Mataimakin Shugaban ISIS da ke ɓoyo a Najeriya —Trump
Abu-Bilal al-Minuki wanda ke zaman ɓoyo a Najeriya ya gamu da ajalinsa a hannun sojojin ƙasar da na Amurka
Sojojin Najeriya da taimakon dakarun Amurka sun yi nasarar kashe Mataimakin Shugaban Kungiyar ISIS na duniya, Abu-Bilal al-Minuki, a wani harin haɗin gwiwa da suka kai a Najeriya.
Da sanyin safiyar Asabar ɗin nan ne Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar cewa haɗin gwiwar dakarun ƙasarsa da na Najeriya sun hallaka Abu-Bilal al-Munki a cikin daren Juma’a.
A sanarwar da Trump ya fitar ta shafin da na Truth Social, ta bayyana cewa Abu-Bilal al-Munki, “Ya ɗauka zai iya ɓoyewa a Afirka, bai san cewa muna da majiyoyi da ke sanar da mu game da abin da yake yi ba.”
Trump ya bayyana cewa, “A cikin daren nan zaratan sojojin Amurka da na Najeriya suka kawar da ɗan ta’addan mafi haɗari a duniya, bayan wani gagarumin tsararren hari.”
Trump, ya miƙa godiyarsa ga gwamnatin Najeriya, inda ya bayyana cewa kashe Abu-Bilal al-Munki zai matuƙar gurgunta shirye-shirye da harkokin ƙungiyar.
“Yanzu ba zai ƙara kai hare-haren ta’addanci a kan ’yan Afirka ko sojojin Amurka. Muna godiya ga gwamnatin Najeriya bisa haɗin gwiwar da ta bayar a wannan aiki,” in ji Trump.
Kawo yanzu dai, hukumomin Najeriya ba su fitar da wata sanarwar game da haɗin ba, duk kuwa da cewa Trump ya bayyana cewa a ƙasar aka kashe Abu-Bilal al-Munki, inda yake zaman ɓuya.
Ƙungiyar ISIS ta samo asali ne daga ƙasar Iraqi kafin ta yaɗu zuwa Syria da wasu ƙasashen Laraba, daga baya ta yi rassa a nahiyar Afirka da suna ISWAP.
Reshen ƙungiyar Boko Haram ya yi bayyana mubaya’a ga ƙungiyar.