Harin Baga: ‘Mun yi tattakin kwana biyu ba abinci’

Wadanda suka gudo daga garin Baga bayan kai harin da Boko Haram suka kai gari a ranar Juma’ar da ta gabata, sun ce sun shafe tsawon kwana biyu suna tafiya a kafa donmi su isa Maiduguri fadar jihar. Kungiyar Boko Haram wadda ta yi mubaya’a ga Kungiyar ISIS, a karkashin Al-Barnawi kuma take gudanar da […]

Harin Baga: ‘Mun yi tattakin kwana biyu ba abinci’

Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima

Wadanda suka gudo daga garin Baga bayan kai harin da Boko Haram suka kai gari a ranar Juma’ar da ta gabata, sun ce sun shafe tsawon kwana biyu suna tafiya a kafa donmi su isa Maiduguri fadar jihar.

Kungiyar Boko Haram wadda ta yi mubaya’a ga Kungiyar ISIS, a karkashin Al-Barnawi kuma take gudanar da ayyukan ta’addancinta a yankin Tafkin Chadi ta kai mummunan hari a garin Baga da ke Karamar Hukumar Kukawa mai tazarar kilomita 200 daga Maiduguri inda ta yi kokarin kwace garin.

Harin ya tilasta jama’a tserewa daga Baga zuwa Maiduguri, bayan da ’yan ta’addan sun kai hari kan cibiyar sojoji ta garin Baga.

Wani mutumin Baga da ya yi gudun hijira zuwa Maiduguri, mai suna Bukar Ali, ya shaida wa Aminiya cewa “Da yammacin ranar Juma’a muka ji karar harbe-harbe tun daga bayan gari, juyawar da za mu yi sai muka ga dandazon mutane da za su haura dubu uku, suna ta kabbarori tare da yin harbe-harbe a sama. Sannan sai wadansu suka nufi barikin sojoji suka yi ta fafatawa da sojojin har cikin dare, mu dai ba mu yi barci ba a ranar.”

Ya kara da cewa “Daga baya sai muka ga jiragen yaki da  helikwaftoci suna shawagi har zuwa Sallar Asuba. Mun yi ta jin amon wutar da jiragen ke saki, ni da iyalina domin ina da mata biyu da ’ya’ya takwas ba mu yi barci ba. Da yin Sallar Asuba ni da iyalina muka yanke shawarar guduwa zuwa Maiduguri, shi ya sa ka ganmu a nan.”

Ya ce “Su ’yan Boko Haram din ba su taba kowa ba cikin fararen hula, balle su kashe shi, saboda tun lokacin da suka shigo suna ta fada mana cewa, “Kada ku ji tsoro, ku tsaya ba za mu taba ku ba, kada ku gudu ba da ku muke yi ba, ba za mu taba ku ba, ku tsaya kada ku gudu! Abin da suke ta fadi ke nan.”

Malama Falmata Modu, ta ce “Mutanen sun shigo Baga amma ba su yi mana komai ba, mun ji tsoro ne ya sa muka tako daga Baga zuwa nan Maiduguri a kasa, duk da yake sun fada mana cewa kada mu gudu ba za su taba mu ba. Mun tako hanya a kasa mun kuma zo da ’ya’ya da jikoki da wasu kayayyakinmu, ba tare da abinci ba. Duk da cewa sun ce ba za su kashe mu ba, amma ba mu yarda da su ba, domin kisa a wurinsu ba komai ba ne, shi ya sa muka kwana biyu muna tafiya a kasa zuwa nan Maiduguri.”

Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Kashim Shettima ya bayyana cewa akwai manyan kalubale da suke fuskantar jihar, musamman lura da yadda ayyukan kungiyar  Boko Haram ke kara ruruwa a jihar.

Gwamna Shettima ya bayyana haka ne a yayin wani taron gaggawa da ya kira a Maiduguri wanda ya samu halartar masu ruwa-da- tsaki a harkar tsaro da suka hada da shugabannin sojoji da na Hukuma DSS da ’yan sanda da sauransu.

Gwamnan ya ce ya kira taron ne domin tattauna matsalolin da ake fama da su a yaki da ta’addanci a jihar tare da lalubo hanyoyi ko matakan magance su. Gwamnan ya ci gaba da cewa za a iya samun nasara ce kawai idan hukumomin tsaro da gwamnati sun yi aiki a matsayin tsintsiya madaurinki daya.

“A yau muna fama da kalubale da dama a Jihar Borno, amma ina fatan kalubalen nan zai kara mana kwarin gwiwa don ganin mun taimaka wa dukan jami’anmu na tsaro, don a kawo karshen Boko Haram. Dukanmu muna da rawar da ya kamata mu taka wajen cimma manufarmu, don haka ya sa na yi taka-tsantsan wajen zabo mahalarta wannan taro, ba wai mun taru nan ba ne don bayyana wane ne mai laifi ko marar laifi ba, domin a ganina ba mu yi wa sojoji adalci ba idan muka taru a nan muka zarge su,” inji shi.

Gwamnan ya jinjina wa kokarin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke yi game da matsalar Boko Haram, inda ya ce ya tabbata Buhari na da niyya, lura da yadda yake hada kan kasashen da ke makwabtaka da Najeriya wajen yaki da Boko Haram.

 

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta