…Harin bam a kasuwar Maiduguri ya ci mutum 56

Mutum 56 ne suka rasu a ranar Talatar da ta gabata, lokacin da wata mota da aka shake da bama-bamai ta fashe a bakin Babbar Kasuwar Maiduguri da ake kira Monday Market.Galibin wadanda suka rasu yara ne da tsofaffin mata da suke sammakon zuwa kasuwar domin sayar da gyada a kofar kasuwar da ’yan kasuwa […]

…Harin bam a kasuwar Maiduguri ya ci mutum 56
…Harin bam a kasuwar Maiduguri ya ci mutum 56

Mutum 56 ne suka rasu a ranar Talatar da ta gabata, lokacin da wata mota da aka shake da bama-bamai ta fashe a bakin Babbar Kasuwar Maiduguri da ake kira Monday Market.
Galibin wadanda suka rasu yara ne da tsofaffin mata da suke sammakon zuwa kasuwar domin sayar da gyada a kofar kasuwar da ’yan kasuwa ke yi suna yin sadaka ga almajirai.
Bam din wanda ya tashi a cikin wata mota kirar fijo mai dauke da buhununan gawayi, ya kuma ci ’yan bangar Sibiliyan JTF tara da fasinjojin da ke jiran bas-bas a gaban wata tashar mota daura da kasuwar, kamar yadda wani ganau ya bayyana.
Kwamandan shiyya ta 3 ta Sibiliyan JTF, Iliya Sa’idu, ya ce “Mutanenmu sun tsaida motar direban bai tsaya ba, sai suka biyo shi tun daga Unguwar London Ciki zuwa Gwange, suka shiga ta Unguwar Doki, suka bulla kasuwar, sai motar ta mace saboda buge mai Keke-NAPEP da ya yi. Ya ce da suka bincike shi ba su gano komai ba ne, sai buhunan gawayi a wurin ajiye kaya, suka tura masa motar, kuma suna cikin tura ta ne sai bam din ya tashi, ya kashe ’yan banga tara da masu wucewa da masu talla.”
Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kashim Shettima, ya yi tir da tashin bam din inda ya ce “Marasa tausayi da imani ne ke aikata haka, kuma da yardar Allah ba za su cimma biyan bukatarsu ba; na yi bakin ciki kwarai da gaske kuma na damu saboda wannan abu ya shafi ’yan bangar da suka sadaukar da kansu wajen taimaka wa jami’an tsaro don kare rayuka da dukiyar al’ummar wannan jiha tamu. Kuma gwamnati za ta ba iyalansu Naira miliyan dai-dai don tallafa musu.”
Kwamishinan ’Yan sandan jihar Alhaji Lawal Tanko ya tabbatar da aukuwar lamarin, kuma ya koka da irin yadda matasa suka far wa ’yan kwana-kwana, ya ce hakan bai kamata ba, domin suna aikinsu ne ba su suka jefa bam din ba.