Harin bam: Bai kamata Jonathan ya jajanta wa Buhari ba – Dokubo

Tsohon Shugaban kungiyar Matasan kabilar Ijaw (IYC), kuma wanda ya kafa rusasshiyar kungiyar Mayakan Sa-Kai ta Neja-Delta (NDPbF) Alhaji Mujahid Asari Dokubo ya soki Shugaba Goodluck Jonathan kan yadda ya yi Allah wadai da harin bam da aka kai ga tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari.Asari Dokubo ya bayyana haka ne a Abuja a ranar […]

Harin bam: Bai kamata Jonathan ya jajanta wa Buhari ba – Dokubo
Harin bam: Bai kamata Jonathan ya jajanta wa Buhari ba – Dokubo

Tsohon Shugaban kungiyar Matasan kabilar Ijaw (IYC), kuma wanda ya kafa rusasshiyar kungiyar Mayakan Sa-Kai ta Neja-Delta (NDPbF) Alhaji Mujahid Asari Dokubo ya soki Shugaba Goodluck Jonathan kan yadda ya yi Allah wadai da harin bam da aka kai ga tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari.
Asari Dokubo ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Talatar da ta gabata, inda ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa shi ya biya wadanda suka yi yunkurin kisan Janar din.
Shugaba Jonathan dai ya la’anci harin da aka kai ga Janar Buhari a ranar Larabar makon jiya a Kaduna a kan hanyarsa ta zuwa Daura a Jihar Katsina. Shugaban ya ce lura da dimbin magoya bayan da Buhari ke da su Najeriya na iya fadawa a cikin rikici inda an samu nasarar hallaka shi.
Dakobu ya ce, “Ina jin abin takaici ne Shugaban kasa ya yi irin wannan kalami. Babban abin takaici ne Shugaban kasa ya rika kambana wani tilon mutum ko mutum biyu a kan fiye da mutum 80 da sauransu da ’yan Boko Hamar suka hallaka. A wurina bai kamata Shugaban kasa ya yi wannan magana ba.”
Dangane da zargin shi ya shirya kashe Janan Buhari, Dokubo ya ce, “Ban biya kowa kudi ba, kuma ban taba biyan wani kudi ba, saboda babu dalilin d azan kashe Buhari. Shi ba wata barazana ba ne gare ni. Shi ba barazana ba ne ga Goodluck, kuma ba na amfani da shafin tiwita.”
Ya ce, ya buga waya ga Daraktan Ayyuka na Hukumar Tsaron kasa (SSS) jim kadan da samun rahoton, inda ya jawo hankalinsa kana bin da ke faruwa. Kuma ya gaya masa cewa lauyansa da shi kansa suna rubuta takardar korafi. “Amma ya shaida min cewa babu wani abu mai kamar haka. Mutumin da aka kama bai ce haka ba,” inji shi.
Game da zargin da ake yi masa na yunkurin wargaza Arewa, Dokubo ya ce, “Duk mun san a zaben shekarar 2011, Goodluck ya fadi a dukkan jihohin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma baya ga Adamawa da Kaduna. Don haka a siyasance Goodluck bai tsammanin kuri’un wadannan jihohi. Kuma za a dauki wadannan jihohi a matsayin makiyansa.”
Ya kara da cewa; “Ni mutumin Ijaw ne, rauni wa mutumin Ijaw daya, rauni ne ga daukacin Ijaw. Kuma zan ci gaba da kare Goodluck Jonathan saboda nid an Ijaw ne. Kuma ba na nadama, ni dan kishin Ijaw ne. Kuna iya kirana dan ta-kefen Ijaw ban damu ba. Amma ku ce ina yi wa Goodluck aiki tsabagen rashin kunya ne, ba na yi wa Jonathan aiki, kuma ni ba dan PDP ba ne.”