Harin bam din Abuja ya shafi ‘yan baro da ‘yan achaba da yawa
Asibitoci a ciki da wajen birnin tarayya Abuja na ci gaba da fuskatar cunkoson jama’a wadanda ke cigiyar ‘yan uwansu bayan tashin bam a cikin garejin manyan motocin bas a garin Nyanya da ke yankin birnin tarayya Abuja a ranar litinin da ta gabata da misalin karfe 6 da rabi na safe, inda mutane da […]

Asibitoci a ciki da wajen birnin tarayya Abuja na ci gaba da fuskatar cunkoson jama’a wadanda ke cigiyar ‘yan uwansu bayan tashin bam a cikin garejin manyan motocin bas a garin Nyanya da ke yankin birnin tarayya Abuja a ranar litinin da ta gabata da misalin karfe 6 da rabi na safe, inda mutane da dama suka rasa ransu.
An ce bam din ya tashi ne a cikin wata karamar mota da ake zargin wadansu ne suka shigo da ita sannan suka sulale suka fice daga cikin garejin, inda wuri ne da motocin safa-safa ke daukar mutane zuwa yankuna daban-daban a cikin kwariyar Abuja.
Wadanda suka rasa rayukansu sun hada da ma’aikata da ’yan Kasuwa da direbobin motoci da yaransu da masu sayar da tikiti da masu sa ido a kan manyan motocin bas-bas (superbisors) da masu tura baro da kuma ’yan achaba masu yawa. Sai kuma wadanda suka tsira da raunuka a cikin masu wucewa.
Wani Direban mota mai suna Judge Ebele da Wakilinmu ya ishe a asibitin Asokoro, wanda ya ce yana aiki da kamfanin sufuri na Edeba line ne da ke da mazauni a garin Benin, ya ce ya dauko fasinja daga garin Lagos zuwa tashar a cikin dare ranar Lahadin da ta gabata kuma yana jiran a yi masa lodi a safiyar ranar litinin din don komawa Legas sai nakiyar ta tashi ta kuma rutsa da shi.“Nan na ga wajen ya cike da kura, sai sannan wuta, ban sake sanin wani abu ba sai bayan da na farfado a wannan Asibitin. Da Ministan Abuja Sanata Bala Muhammad da ya ziyarci Asibitin a ranar Talata , ya bada umarnin a dauke wannan mutumin zuwa wani asibiti na musamman saboda mummunar kunar da ya yi.
Shi ma wani mai suna Adeoye Busayo da ke kwance a wani dakin daban a asibitin na Asokoro, ya shaida wa wakilinmu cewa, “ ina wucewa ta titin da ke daura da garejin a cikin motata tare da wadansu makwabtana uku da na dauka, sai na ji mummunar kara tare da girgiza. Gilasan motata daga ko wane bangare sun tarwatse, sannan rufin motar ya yiwo kasa har ya danne min kai. Bayan jimawa kadan na yunkuro na fito ta taga, kuma ina jin na samu wadannan raunukan ne daga ragowar gilashin da ke jikin motar a lokacin da nake kokarin fitowa ta tagarta, sai dai ban san halin da abokan tafiyata suke ciki ba.’’
Adeoye wanda ya ce yana gudanar da kamfanin bada shawara a kan harkan tsaro ne, ya ce yana kan hanyarsa ta zuwa cikin kwariyar Abuja ne lamarin ya rutsa da shi.
Shi kuwa Usman Yunusa, wanda yake da zama a garin Karu site Abuja, ya ce yana wucewa ne a kan babur dinsa sai ya ji karar fashewar nakiyar, “nan na fadi kasa na samu lokaci mai tsawo ba na jin komai a kunnena, har dai lokacin da aka tallafo ni aka sanya ni a cikin wata mota zuwa wannan Asibitin, inda na ke samun sauki. Da ya ke zantawa da manema labarai bayan kammala zagaya dakunan da aka kwantar da wadansu daga cikin wadanda suka tsira da raunukan a asibitin Asokoro, ministan Abuja Sanata Bala Muhammad, wanda yana kasar Saudiyya a lokacin da lamarin ya faru ya yanke ziyarar ya dawo, ya bayar da umarnin a kula da majinyatan kyauta a daukacin asibitocin gwamnati da kuma masu zaman kansu da ke yankin, sannan ya bayyana alhininsa a kan abin da ya faru.
Wata majiya a Kamfanin sufuri na Abuja Urban Mass, ta shaida wa Aminiya cewa, direbobi hudu na kamfanin sun rasa ransu a yayin tashin nakiyar, sai kuma ma’aikata 16 da suka samu raunuka, a yayin da wadansu ma’aikatan kamfanin kuma ba a gansu ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoton. Haka kuma majiyar ta ce akwai kuma wadanda suka rasu daga cikin masu aiki a bangaren tikiti da ke aiki da wani kamfani da ke hulda da su.
Shi dai wannan garejin ya fara aiki ne a ranar 18 ga watan Janairu na wannan shekarar bayan far aiki da dokar hana kana motocin bas-bas zuwa cikin kwariyar birnin Abuja. Garejin yana karkashin kulawar wani kamfani ne, wanda yake amsar kudi daga wajen kananan bas-bas da kananan motoci da ke lodi a wajen, a matsayin kudin shiga.
A ranar Talata direbobi da wadansu ma’aikatan kamfanin sun gudanar da zanga-zanga a harabar kamfanin, inda suka bukaci kamfanin da ya yi wani abu ga iyalan direbobi da kumaa sauran ma’aikata da suka rasu, da kuma masu jinya, sannan a biya su albashinsu na watan da ya wuce. Daga bisani dai an shawo kansu bayan zantawa da jagororinsu, inda aka tattauna a kan al’amarin.
’Yan Najeriya sun caccaki Jonathan kan tikar rawa a lokacin da ake makoki
Daga Salihu Makera
’Yan Najeriya sun mayar da martani cikin fushi kan yadda Shugaban kasa Godluck Jonathan ya rika tika rawa a lokacin da ya ziyarci Kano don karbar tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau zuwa Jam’iyyar PDP kwana daya da kashe sama da mutum 70 da raunata daruruwa a harin bam na Nyanya da ke wajen Abuja.
“Rashin kan gado ne, rashin hankali ne, abin takaici ne, halin mugunta ne,” su ne wasu daga cikin kalmomin da aka yi amfani da su wajen bayyana ziyarar siyasar ta Shugaban kasa a Kano.
“Mu fadi gaskiya, shin ya dace a matsayinsa na uba, Shugaban kasa ya tiki rawa a gangamin taron jam’iyyar kwana daya da aukuwar harin?” inji Betty Abah, wata ’yar jarida mai rajin kare hakkin jama’a, kuma ta kara da cewa: “Me zai faru idan ya tura wakili yayin da zai zauna ya nuna kamar yana ganawa ne da hafsoshin tsaro? Ko da bai damu ba, yin haka daidai ne ga mutuncinsa? Wane irin sako yake isarwa ga jama’a? Ya yi haka a lokacin bikin cikar Najeriya shekara 100. Wane irin bayani zai yi kan irin wannan rashin kan gado?”
Shi kuwa Bamidele Aturu, lauya mai kare hakkin jama’a, cewa ya yi: “Wannan tsabagen rashin kan gado ne. Kuma wata manuniya ce cewa shugabannin wannan kasa ba su dauki rayukanmu da muhimmanci ba ko kadan.” Ya kara da cewa: “Mahara sun kashe sama da mutum 200, amma kasa da awa 24 Shugaban kasa ya tafi Kano taron siyasa. Wannan yana nuna ba su dauke mu da muhimmanci ba, rayukanmu ba komai ne a wurinsu ba. Wannan shi ne tsabagen rashin tunani da na taba gani a wannan lokaci. Ba zai rasa komai ba idan ya dage kamfen din da wata daya ko biyu, domin ya karfafa gwiwar wadanda suka rasa ’yan uwansu su farfado daga jimamin harin.”
Mista Aturu ya ce tabargazar Shugaban kasa ta nuna babban gibin da ke tsakanin ’yan Najeriya da shugabanninsu na siyasa, wadanda ya ce sukan bukaci talakawa ne kawai don su hau kujerar mulki. Ya ce abin da Shugaban kasa ya yi in a wata kasar ce ya kai ya rasa kujerarsa.
“Irin haka ba zai faru a wani wurin ba. A sauran kasashe ana iya tsige Shugaban kasa kan abin da (Jonathan) ya yi. Abin tashin hankali ne. A ce ya yi tafiyar nan ya nuna cewa a wurinsa siyasa ta fi rayukan ’yan Najeriya muhimmanci,” inji Aturu.
Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso na Jihar Kano kuwa cewa ya yi a lokacin da Najeriya ke zaman makokin mutanen da harin bam na Nyanya sai ga Shugaban kasar yana yawo marar amfani.
“A daidai lokacin da rayuka da dama suka salwanta, mutane da dama ke kwance a gadajen asibiti suna bukatar taimakon jini domin su rayu, sai ga Shugaban kasa yana zagaya kasa da sunan gangamin PDP,” inji Kwankwaso a wurin bikin rantsar da daliban Jami’ar Arewa maso Yamma da ke Kano.
“Wannan rashin tunani da rashin hankali ne,” inji Lauya Festus Keyamo.
“Wannan alama ce da ke nuna gwamnati ba ta dauki ran ’yan Najeriya da kima ba. A zahiri ma wannan na tabbatar da cewa wannan gwamnati na ji dadin kashe-kashen da ke gudana a wannan sashi na kasar nan. Abin Allah wadai ne a ce Shugaban kasa ba zai iya ayyana rana daya domin zaman makoki ba, alhali mun rasa kusan rayuka 200,” inji Shugaban kungiyar CACOL, Debo Adeniran.
Kuma ya zargin Shugaban kasar da cewa yana jin dadin ya ga jini yana zuba, kuma bai damu ba, domin ya taba fadin cewa bai damu da abin da ‘’yan Najeriya suka fada game da shi ba.