Harin bam: Hukumar NEMA ta tallafa wa Jihar Gombe

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) ta hannun shugabanta Malam Muhammad Sani Sidi, ta ba Jihar Gombe tallafin magunguna na miliyoyin Naira don agaza wa wadanda harin bam na tashar motar Dukku ya rutsa da su a ranar 22 ga Disamban 2014.Da yake karbar maganin a madadin gwamnatin jihar, Ministan Sufuri Sanata Abdullahi Idris […]

Harin bam: Hukumar NEMA ta tallafa wa Jihar Gombe
Harin bam: Hukumar NEMA ta tallafa wa Jihar Gombe

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) ta hannun shugabanta Malam Muhammad Sani Sidi, ta ba Jihar Gombe tallafin magunguna na miliyoyin Naira don agaza wa wadanda harin bam na tashar motar Dukku ya rutsa da su a ranar 22 ga Disamban 2014.
Da yake karbar maganin a madadin gwamnatin jihar, Ministan Sufuri Sanata Abdullahi Idris Umar, ya nemi gwamnatin jihar ta ci gaba da hada kai da Gwamnatin Tarayya
don samun tallafin agajin gaggawa a kan lokaci.
Ministan ya ce tallafin magunguna umurni ne da Shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya ba Hukumar NEMA ta jihar don tallafa wa wadanda harin bam din ya shafa.
Sanata Idris Umar, ya yi kira ga jama’ar kasar nan su kasance masu sanya ido da kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba ga hukuma.
Malam Sani Sidi, ya yi wa al’ummar jihar ta’aziyya da jaje kan wannan bala’i na harin bam da ya faru, wanda ya yi sanadiyar asarar rayuka masu yawa.
Babban Likitan Asibitin kwararru na Jihar wanda ya karbi magungunan daga Ministan Dokta Reuben Ardo Maifartanya ya ce lokacin da lamarin an kai gawar mutum 19, biyu da maza 17.
Dokta Reuben, ya ce washegari daya daga cikin wadanda suka ji rauni ya rasu, bayan kwana hudu wani ma ya sake rasuwa, wadanda suka samu rauni an sallame su saura mutum daya.

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista