Harin bam: Wata mata ta haihu kafin lokacin haihuwarta saboda firgici
Harin kunar bakin wake da aka kai a tashar motar Dadin Kowa da ke Gombe a ranar Talatar makon jiya ya firgita wata mace mai suna Mary Emmanuel mai shekara 30 ta haife cikinta dan wata takwas. Misis Mary Emmanuel tana kan hanyarta ta dawo gida daga wajen aiki a kan babur ne wannan hari […]
Harin kunar bakin wake da aka kai a tashar motar Dadin Kowa da ke Gombe a ranar Talatar makon jiya ya firgita wata mace mai suna Mary Emmanuel mai shekara 30 ta haife cikinta dan wata takwas.
Misis Mary Emmanuel tana kan hanyarta ta dawo gida daga wajen aiki a kan babur ne wannan hari na kusa da unguwarsu ya faru, kuma jin karar fashewar bam din ya firgita.
Majiyarmu ta ce tun daga lokacin da ta firgita har yanzu ba ta san inda hankalinta yake ba kuma ganin cewa ta bugu har kanta ya samu matsala ya sa likitoci suka yi shawarar yi mata aiki a cire mata dan dake cikinta.
Wakilinmu ya ziyarci Asibitin kwararru na Gombe don ganawa da Mary, amma ya iske an mayar da ita Asibitin Tarayya inda aka kai danta aka saka shi a kwalba.
Kuma saboda tana cikin mawuyacin hali mijinta Emmanuel Abraham ne ya yi masa karin haske kan yadda lamarin ya faru.
Emmanuel Abraham, ya ce matarsa tana cikin mawuyacin hali amma yana da karfin gwiwar cewa Allah zai ba ta lafiya kuma dan da aka cire mata yanzu haka yana nan lafiya sai dai likitoci sun sa shi a kwalba ne saboda an cire shi bai yi kwari ba.
Ya ce matarsa tana kan babur ne da ta ji karar fashewar bam din a kwanar shiga unguwarsu ta Nasarawo ta razana ta fado daga kan babur din har kanta ya fashe inda likitoci suka ce kwakwalwarta ta tabu sai dai suna da kwarin gwiwar komai zai daidaita.
Emmanuel Abraham, ya ce lokacin da aka kai ta asibiti ya yi tafiya amma da ya dawo aka gaya masa abin da ya faru har an kai mai dakinsa asibiti. Ya ce matar tasa tana aiki da wata kungiya da ba ta gwamnati ba mai suna Chat.