Harin bam ya halaka sojojin Masar a Sinai
Mutum 10 sun halaka a harin bam yayin da dama suka samu raunuka a wani harin bam da aka kai wa sojojin Masar a garin el-Arish da ke birnin Sinai da ke Arewacin kasar shekaranjiya Laraba.Jaridar Al-Masri al-Youm ta ce wani ayarin bas-bas da ke dauke da sojojin kasa ya hadu da harin bam da […]
Mutum 10 sun halaka a harin bam yayin da dama suka samu raunuka a wani harin bam da aka kai wa sojojin Masar a garin el-Arish da ke birnin Sinai da ke Arewacin kasar shekaranjiya Laraba.
Jaridar Al-Masri al-Youm ta ce wani ayarin bas-bas da ke dauke da sojojin kasa ya hadu da harin bam da aka dasa a gefen hanyya a lokacin da ya nufi yankin Kahrouba. Kuma bayanai sun nuna akwai yiwuwar wadanda suka mutu su karu.
Hare-hare ga jami’an tsaro sun karu a Masar sakamakon kawar da Shugaba Muhammed Mursi mai ra’ayin Musulunci a watan Yuli. Sai dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin bam din, a kasar da take fama da rashin tabbas a ’yan shekarun nan, lamarin da ya karu bayan faduwar Shugaba Hosni Mubarak.
Kawar da shi a Fabrairun 2011 ya bar Arewacin Sinai a hannun kungiyoyin masu jihadi, wasu da suke da alaka da yankin Zirin Gaza. Kuma a watan Satumba da ya gabata sojoji sun kaddamar da farmaki kan masu dauke da makamai a Sinai, amma suka hadu da munanan hare-haren bama-bamai. Sannan a kwanakin baya jami’an tsaro 100 aka kashe a kasar.
Harin na ranar Laraba da ya auku da misalin karfe 7:45 na safe a kan hanyar Rafah zuwa el-Arish ana jin shi ne mafi muni tun kawar da Shugaba Mursi. Kuma daga cikin mutum 10 da suka halaka shida sojoji ne, uku jami’an tsaro daya kuma direba, kamar yadda sojojin kasar suka ce, sai kuma sojoji 35 da suka samu rauni a harin da ya shafi daya daga cikin bas-bas din.
Sojojin suna dawowa Alkahira ne bayan aikin lalata wani mashigi da ke shiga Zirin Gaza, kuma an dauki wadanda suka munanan rauni a jirgin sama zuwa birnin kasar.
Firayi Ministan kasar Hazem Beblawi ya la’anci harin inda ya ce gwamnati za ta dauki matakan da suka dace don dakile hare-haren ’yan ta’adda.
Wata majiya a kasar ta ce harin daukar fansa ce kan harin da sojojin suka kai mazaunin ’yan bindiga inda suka kwace musu makamai.
A farkon wannan mako wata kungiya mai suna Ansar Bayt al-Makdis ta harbe wani babban jami’in tsaron kasar mai suna Kanar Mohammed Mabruk da aka shirya zai ba da shaida a shari’ar da ake yi wa Mursi.