Harin bama-bamai: Yau za a ci gaba da gasar rukunin Faransa
A yau Juma’a ne ake sa ran za a cigaba da gudanar da gasar rukuni-rukuni na Faransa da aka fi sani da Ligue 1 bayan hare-haren bama-bamai da aka kai birnin Paris a ranar Juma’ar da ta wuce inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. A karshen makon jiya ne dai hukumar shirya wasanni […]
A yau Juma’a ne ake sa ran za a cigaba da gudanar da gasar rukuni-rukuni na Faransa da aka fi sani da Ligue 1 bayan hare-haren bama-bamai da aka kai birnin Paris a ranar Juma’ar da ta wuce inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
A karshen makon jiya ne dai hukumar shirya wasanni ta Faransa ta soke dukkanin wasannin da aka shirya bayan harin bama-baman. Akalla mutane 129 ne suka rasu a harin bam din yayin da wasu da dama suka jikkata.
daya daga cikin harin an yi shi ne a filin wasa na Stade de France a lokacin da aka gudanar da wasan sada zumunta a tsakanin Jamus da Faransa.
“A wannan mako za a cigaba da gasar rukuni-rukuni ta Faransa”, kamar yadda Ministan wasanni Theiry Brillard ya sanar a ranar Talatar da ta wuce.
Sai dai Ministan ya ce za a dauki kwararan matakan tsaro a ciki da wajen filayen wasannin don kauce sake aukuwar kai hare-hare ga ’yan ta’adda.
Mai rike da kofin gasar rukunin Faransa Paris Saint Germain (PSG) a gobe Asabar ne za ta kara da Lorient a cigaban gasar.