Harin birrai ya tilasta mazauna Japan yawo da almakashi
Mahukunta a Arewacin kasar Japan sun bazama farautar wasu birrai da suka yiwa mutane 50 rauni. Wani jami’i da ya nemi a sakaya sunansa ya ce guda daga ciki birran ya shiga hannu har sun aika shi lahira, sai dai sauran 49 na watse a yankin. Ya Kashe Mahaifinsa Kan Kyautar Fili Dubun barauniyar jaririyar […]
Mahukunta a Arewacin kasar Japan sun bazama farautar wasu birrai da suka yiwa mutane 50 rauni.
Wani jami’i da ya nemi a sakaya sunansa ya ce guda daga ciki birran ya shiga hannu har sun aika shi lahira, sai dai sauran 49 na watse a yankin.
Hukumomi a birnin Yamaguchi dai sun jima suna fakon birran da suka addabi mutane da cizo da yakushi, ba babba ba yaro.
Jami’in ya ce a ranar Talata ne aka tattaro wasu mafarauta na musamman suka kamo daya daga cikin birran yana gararamba a kusa da tabkin da ke wata makaranta a Yamaguchin.
“Shaidu sun fada mana birran ba girmansu daya ba, kuma duk da mun kama wanda muka gani, mun ci gaba da samun rahotannin wasu hare-haren birrai,” in ji shi.
Wannan lamari dai ya tilasta wa al’ummar birnin yawo da lema mai tsini, da almakashi mai kaifi domin gudun kada birran su yi musu kwanton bauna.