Harin Boko Haram: Mutanen Magumeri sun samu tallafi
Al’ummar da harin kurgiyar Boko Haram ya shafa a Karamar Hukumar Magumeri ta Jihar Borno sun amfana da kayan tallafin rage radadi. A ‘yan kwanakin nan mutanen garin sun yi fama fa da hare-haren kungiyar, wanda ya yi sanadiyyar kone babban asibitin garin da wasu muhimman gine-ginen gwamnati. Yayin wata ziyawar jajantawa da ya kai […]
Al’ummar da harin kurgiyar Boko Haram ya shafa a Karamar Hukumar Magumeri ta Jihar Borno sun amfana da kayan tallafin rage radadi.
A ‘yan kwanakin nan mutanen garin sun yi fama fa da hare-haren kungiyar, wanda ya yi sanadiyyar kone babban asibitin garin da wasu muhimman gine-ginen gwamnati.
Yayin wata ziyawar jajantawa da ya kai musu, wakilin Magumeri a Majalisar Wakilai, Hon. Usman Zannah ya gwangwaje su da kabakin arziki domin rage musu radadi tare da addu’ar dawowar zaman lafiya a yankin da ma kasa baki daya.
Kayan da aka raba musu sun hada da buhunan gero 830, na shinkafa 830, na garin masara 833, na dawa 166, katan din taliya 166, buhun suga 56, kwali 330 na tumatirin gwangwani, galan 166 na man girki sai kuma katan 260 na fakitin kafi-zabo.
Sauran kayan sun hada da katifu, barguna, gidajen sauro da tabarmi guda 600 kowanne, tukwanen girki 160, zannuwa turame 330, kayan yara 600 sai kuma bokitan roba guda 500.
Da yake jawabi yayin karbar kayayyakin a madadin al’ummar yankin, Dagacin Magumeri, Abba Fari Shehu Abubakar Garbai ya yaba wa dan majalisar kan tallafi da kuma jajantawar.
Ya kuma ce za su tabbatar an raba kayan ga wadanda suka fi bukata, tare da kira ga sauran masu hannu da shuni da su tallafa wa al’ummar yankin kasancewar akasarinsu yanzu suna bukatar taimakon.