Harin Boko Haram na garin Gaidam ya tilasta jama’a hijira zuwa Nijar
Harin ’yan Boko Haram a garin Gaidam da ke Jihar Yobe a makon jiya da ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi na milyoyin Naira tare da kone babbar kasuwar garin ya tilasta dubban jama’a yin hijira zuwa garin Maine Sarua da ke Jihar Difa a Jamhuriyar Nijar.Wakilinmu wanda ya ziyarci garin na Maine Sarua a […]

Harin ’yan Boko Haram a garin Gaidam da ke Jihar Yobe a makon jiya da ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi na milyoyin Naira tare da kone babbar kasuwar garin ya tilasta dubban jama’a yin hijira zuwa garin Maine Sarua da ke Jihar Difa a Jamhuriyar Nijar.
Wakilinmu wanda ya ziyarci garin na Maine Sarua a Nijar a karkashin tawagar Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam, ya ce Gwamnan ya jajanta wa ’yan gudin hijirar dangane da bala’in da ya auka musu, inda ya yi alkawarin gwamnatin jihar za ta tallafa musu.
Kafin Gwamnan ya isa Maine Sarua ya tsaya a garin Gaidam don ganin irin barnar da maharan suka yi, inda suka kone matsugunin sojojin rundunar tsaro ta JTF da gidaje biyar da ofishin shiyya na ’yan sanda da ba a dade da gyara shi ba, saboda kone shi a baya da maharan suka yi. Kuma Gwamnan ya ziyarci babbar kasuwar Gaidam da daya ce daga cikin manyan kasuwannin dabbobi da amfanin gona da maharan suka kone ta. Sai dai ya roke su kan su guji zurmuke kan asarar da suka yi.
Alhaji Ibrahim Gaidam wanda shugaban kasuwar Alhaji Ba-Mala Usman ya zaga da shi harabarta ya tabbatar wa al’ummar garin cewar da zarar ya koma za a turo musu da kayan abinci don rage musu radadi ta hannun Hukumar Bada Tallafin Gaggawa (SERA).
Al’ummar garin sun bayyana rashin jin dadinsu kan yadda jami’an tsaro suka gudu suka bar su a yayin harin, wanda hakan ne ya yi sanadin muguwar barnar da aka yi musu.
Daga Gaidam ne tawagarsa ta suka kunshi jami’an gwamnati da Mai martaba Mai Ngazargamu Alhaji Tijjani Saleh Gaidam da jami’an tsaro ta tafi garin Maine Sarua inda Gwamnan ya hadu da takwaransa na Difa Alhaji Yakubu Usman suka zarce garin Maine don ganawa da dubban jama’ar da suka samu mafaka a can.
A jawabinsa ga wadanda suka samu mafaka a Maine Sarua, Gwamna Gaidam ya gode wa gwamnatin Jamhuriyar Nijar da ta Jihar Difa da mahukuntan garin bisa karimcin da suka nuna wa al’ummarsa.
Ya kuma roki masu gudun hijirar su yi kokarin komawa gidajensu gwamnatinsa za ta tallafa musu.
Gwamnan Jihar Difa Alhaji Yakubu Usman ya ce yanzu haka sun karbi ’yan gudun hijira daga Gaidam ga Kanemma sama da dubu hudu, inda gwamnatin jihar take daukar nauyin mutum 1,385 da aka samar musu masaukai da abinci.