Harin Boko Haram ya ci ma’aikacinmu
Hare-haren da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne suka kai garin Damaturu a ranar Alhamis din makon jiya ya rutsa da daya daga cikin ma’aikatan kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Weekly Trust da Sunday Trust da kuma Aminiya Malam Abdulwasiu Akinsanya. Matar marigayin da suke tafiya tare Malama Bilkisu A. […]
Hare-haren da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne suka kai garin Damaturu a ranar Alhamis din makon jiya ya rutsa da daya daga cikin ma’aikatan kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Weekly Trust da Sunday Trust da kuma Aminiya Malam Abdulwasiu Akinsanya. Matar marigayin da suke tafiya tare Malama Bilkisu A. Akinsanya ta ce maharan sun kashe marigayin ne da misalin karfe 5.30 na yamma lokacin da motarsu ta lalace kusa da shingen bincikar motoci na sojoji da ke kusa da gidan mai na kamfanin mai na NNPC MEGA STATION gab da lokacin da maharan za su kawo hari ga shingen. Malama Bilkisu ta ce lokacin da ’yan bindigar suka harbe maigidanta tana tare da shi da ’ya’yansu a kan hanyarsu ta zuwa Kano, daga bisani jami’an tsaro sun dauki gawar marigayin zuwa asibitin Damaturu su kuma suka samu mafaka a ofishin ’yan sanda na C. Dibision da ke Maisandari. Kafin rasuwar marigayin yana aiki ne a bangaren buga jaridu na ofishin shiyya na kamfanin da ke Maiduguri. An haifi marigayi Abdulwasiu ne a ranar 24 ga Janairun 1974, ya fara aiki da kamfanin Media Trust a watan Satumban shekarar 2010, bayan ya baro Kamfanin Buga Jaridun New Nigerian da ke Kaduna, a matsayin babban jami’I a fanni dab’i da kuma kwamfuta. Babban Manajan Kula da Ma’aikata na Kamfanin Media Trust Malam Alhassan Yusuf ya bayyana kashe Abdulwasiu a matsayin babban abin bakin ciki, kuma babban rashi ga kamfanin da iyalansa, yayi addu’ar Allah Ya sa Aljannar Fiddausi ce makomarsa.