Harin Boko Haram ya kashe mutum 38 a Nijar

A jiya Alhamis ne hukumomi a Jamhuriyar Nijar suka ce ‘yan kungiyar Boko Haram sun kashe akalla mutane 38 a lokacin da suka kai hari a kauyuka biyu da ke kudancin kasar. dan majalisar dokokin da ke wakiltar yankin, Bulu Mammadu ya shaida wa BBC cewa an kai harin ne a garuruwan Ungumawo da Lamina […]

Harin Boko Haram ya kashe mutum 38 a Nijar
Harin Boko Haram ya kashe mutum 38 a Nijar

A jiya Alhamis ne hukumomi a Jamhuriyar Nijar suka ce ‘yan kungiyar Boko Haram sun kashe akalla mutane 38 a lokacin da suka kai hari a kauyuka biyu da ke kudancin kasar.

dan majalisar dokokin da ke wakiltar yankin, Bulu Mammadu ya shaida wa BBC cewa an kai harin ne a garuruwan Ungumawo da Lamina da ke Jihar Diffa.
Har ila yau, ya ce ‘yan kungiyar sun cinna wa mata da yara wuta cikin gidaje, sannan suka kona wasu sassan garuruwan. dan Majalisar ya yi kira ga hukumomin jihar su dauki kwararan matakan dakile irin wadannan hare-haren.
kasashen Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru da kuma Jamhuriyar Benin sun sha alwashin hada hannu wajen yaki da Boko Haram.
Jamhuriyar Nijar dai ta sha fuskantar hare-haren Boko Haram tun lokacin da ta shiga cikin wadannan kasashen da suka daura aniyyar yaki da kungiyar, kuma ko a karshen watan Afrilun da ya wuce, sojin kasar 48 ne suka rasa rayukansu lokacin da ‘yan kungiyar suka kai hari a tsibirin Karamga, matsugunin sansanin sojin kasar.