Harin Boko Haram: Zulum ya kai ziyarar jaje garin Darajamal
Gwamnan ya bayyana takaicinsa kan yadda ‘yan ta’addan suka mutane a ƙauyen.
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ziyarci garin Darajamal da ke Ƙaramar Hukumar Bama, domin jajanta wa iyalan mutanen da Boko Haram suka kashe.
Rahotanni sun nuna cewa ’yan ta’addan Boko Haram sun hallaka aƙalla mutum 63, yayin da dakarun soja suka kashe 30 daga cikinsu.
- Tsadar Rayuwa: NLC ta buƙaci gwamnati ta sake duba albashin ma’aikata
- Najeriya ce ƙasa ta biyar mafi yawan Musulmai a duniya
Da yake magana da mazauna garin Zulum ya ce: “Abin takaici ne sosai. An dawo da wannan al’umma nan ba daɗewa, amma sai ga shi an sake fuskantar mummunan hari a daren jiya.”
Gwamnan ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ƙara ƙarfafa jami’an tsaro a dazuka, inda ya bayyana cewa akwai buƙatar ƙara yawan sojoji domin kare rayukan jama’a yadda ya kamata.
Idan ba a manta Aminiya ta ruwaito yadda maharan suka farmaki ƙauyen, inda suka kashe gomman mutane.