Harin bom ya kashe mutane a Maiduguri

Mutum biyu sun mutu wasu kuma sun jikkata a harin na jajibirin Babbar Sallah

Harin bom ya kashe mutane a Maiduguri

Tsohon hoto.

Akalla mutum biyu sun mutu wasu da dama kuma sun jikkata baya fashewar wasu abubuwa da ake kyautata zaton bamabamai ne a garin Maiduguri, Jihar Borno.

Shaidu sun ce sama da mutum goma sun samu raunuka sakamakon fashewar bom din a jajibirin Babbar Sallah.

Shaidun sun ce abubuwan da suka fashe rokoki ne aka harko daga inda ba a iya tantacewa ba.

Hakan ta faru ne a yankin Custom da ke kan hanyar Tashan Bama bayan la’asar.

Harin na zuwa ne a washegarin ranar da matakan kungiyar Boko Haram suka kai wa ayarin motocin Gwamna Babagana Zulum na jihar hari.

Kungiyar wadda ta shafe shekara 12 tana tayar da kayar baya ta kai wa motocin gwamnan farmaki ne a hanyarsa ta zuwa raba abinci ga ‘yan gudun hijira a Monguno da Baga.