Harin bom ya kashe mutum 18 a masallaci a Afghanistan

Ana fargabar yiwuwar samun karuwar wadanda za su iya mutuwa sakamakon tashin bom din.

Harin bom ya kashe mutum 18 a masallaci a Afghanistan

Akalla mutum 18 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon wani mummunan harin bom da ya auku a wani masallacin Juma’a a Yammacin kasar Afghanistan.

Wani bidiyo da a yanzu ya karade kafofin sadarwa ya nuna gawarwakin mutane barbaje a harabar masallacin yayin da jini ya zama tamkar abun shimfida a daben masallacin.

Kakakin gwamnatin birnin na Herat, Hameedullah Motawakkel ya ce baya ga mutum 18 da suka mutu a harin akwai kuma wasu 21 da suka samu muggan raunuka wadanda tuni aka mika su ga asibiti mafi kusa.

Daga cikin wadanda suka mutu sakamakon harin a masallacin Guzargah da ke a birnin Herat har da wani fitaccen malami addinin Islama daya daga cikin ’yan gaba-gaba masu goyon bayan gwamnatin Taliban, Mujib-ul Rahman Ansari.

Mujib-ul Rahman Ansari shi ne wanda a farkon wannan shekara ya yi kiran da a fille kan duk wani da ya karya dokar gwamnatin Afghanistan ta yanzu komai kankanta.

Kakakin gwamnatin Taliban, Zabihullah Mujahid da ke tabbatar da kisan Mujib-ul Rahman a harin na Juma’ar nan, ya bayyana fitaccen malamin a matsayin wanda ya yi shahada.

Bayanai sun ce ana fargabar yiwuwar samun karuwar wadanda za su iya mutuwa sakamakon tashin bom din.

A baya bayan nan dai an samu saukin tashin husuma a Afghanistan tun bayan karbe gwamnati da Taliban ta yi a bara, sai dai ana ci gaba da samun tashin boma-bomai nan da can; lokaci zuwa lokaci.

A watan da ya gabata, wani harin bom da kungiyar IS ta dauki alhakin kai wa wani masallaci a birnin Kabul, ya kashe wani malami da ke goyon bayan gwamnatin ta Taliban.