Harin Borno: Mun kashe ’yan ta’adda 34, mun rasa dakaru 6 – Sojoji
Sai dai, sojoji shida sun rasa rayukansu a fafatawar da ta faru a ranar Asabar.
Rundunar Sojin Najeriya, ta tabbatar da kisan ’yan ta’adda 34, a yayin wata arangama da sojoji suka yi a Sabon Gari da ke Ƙaramar Hukumar Damboa a Jihar Borno.
Sai dai, sojoji shida sun rasa rayukansu a fafatawar da ta faru a ranar Asabar.
- Radda ya yi wa Kwamishinoni sauyin ma’aikatu a Katsina
- Sojoji da dama sun ɓace bayan harin Boko Haram a Borno
Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar, Manjo-Janar Edward Buba ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.
Ya bayyana cewa ’yan ta’addan, da suka zo a kan babura da motoci ɗauke da muggan makamai, sun yi yunƙurin kai wa sojoji hari domin ɗaukar fansar kashe shugabansu da dakarunsu.
Ya ce, “Dakarunmu tare da taimakon JTF da ’yan sa-kai sun daƙile harin.
“Jiragen yaƙin Operation HAƊIN KAI ta kuma hallaka wasu da suka tsere, inda aka ƙwato bindigogi AK-47 guda 23 da harsasai sama da 200.”
Ya ƙara da cewa dakarun sun samu ɗauki duk da cewa Kwamandan ’yan sa-kai ya ji rauni sakamakon fashewar bam.
Ya ce, “Adadin ’yan ta’adda 34 aka kashe, amma abin takaici, mun rasa jaruman sojoji shida a wannan fafatawa.”
Manjo-Janar Buba, ya kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su mutunta tsarin sanar da iyalan waɗanda suka rasu kafin fitar da sunayensu a hukumance.