Harin da sojoji ke kai wa masu zanga-zanga a Masar ya rage musu magoya baya

Mutuwar mutum sama da dubu da 200 a farmakin da jami’an tsaron Masar suka kai wa magoya bayan hambararren shugaban Masar Muhammad Mursi, ya rage musu magoya baya. Wasu daga cikin wadanda suka goyi bayan juyin mulkin da aka yi a watan da ya wuce, sun fara nuna rashin gamsuwarsu da gwamnatin riko da sojoji […]

Harin da sojoji ke kai wa masu zanga-zanga a Masar ya rage musu magoya baya
Harin da sojoji ke kai wa masu zanga-zanga a Masar ya rage musu magoya baya

Mutuwar mutum sama da dubu da 200 a farmakin da jami’an tsaron Masar suka kai wa magoya bayan hambararren shugaban Masar Muhammad Mursi, ya rage musu magoya baya. Wasu daga cikin wadanda suka goyi bayan juyin mulkin da aka yi a watan da ya wuce, sun fara nuna rashin gamsuwarsu da gwamnatin riko da sojoji suka kafa.
“Al’amarin da ke faruwa a halin yanzu masifa ce kawai,” a cewar Walid Osman, wani manajan sarrafa kudi a wani kamfani mai zaman kansa. Osman ya kasance daya daga cikin wadanda suka yi zanga-zangar 30 ga watan Yuni, a halin yanzu ya koma cikin magoya bayan Mursi, kamar yadda ya bayyana wa shafin sadarwar Aljazeera.
Akwai yiwuwar wannan gwamnati ta hadu da cikas, domin babban Limamin Al-Azhar el-Tayyep ya nisant akansa da Gwamnatin rikon, tun bayan da ta kaddamar da kisa a kan magoya bayan Mursi, ta kama na kamawa ta daure. Uwa-uba murabus din Muhammad ElBaradei daga cikin gwamnatin shi ma wani cikas ne.
kungiyar ’yan Uwa Musulmi ta Masar na fuskantar adawa daga kasashen Larabawa, ta yadda duk wanda ya nuna yana kaunarsu, ko tausaya musu, to ya gamu da tasku. Alal misali, kwananan kafofin yada labarai suka ruwaito hamshakin attajirin Saudiyya, Alwaleed bin Talal ya kori Shugaban gidan talabijin dinsa na AlRisala daga aiki, saboda ya nuna goyon bayansa ga kungiyar Ikwan ta Masar. Malamai masu wa’azi ma ba a kyale su ba, domin an dakatar da wani malami a kasar Kuwait.