Harin da ’yan ta’adda suka kai filin jirgin sama ya yi ajalin sojoji 11 a Nijar

Tun da safiyar Alhamis ne mazauna Yamai suka wayi gari da ƙarar harbe-harbe a yankin filin jirgin saman.

Harin da ’yan ta’adda suka kai filin jirgin sama ya yi ajalin sojoji 11 a Nijar

Ma’aikatar Tsaron Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da harin da wasu ’yan ta’adda suka kai Filin Jirgin Sama na Diori Hamani da ke Yamai, babban birnin ƙasar, a ranar Alhamis.

A cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na ƙasar, ma’aikatar ta ce sojoji 11 da fararen hula biyu sun rasa rayukansu sakamakon harin, yayin da dakarun tsaro suka kashe ’yan ta’adda 22 a artabun da ya biyo baya.

Sanarwar ta ce tuni jami’an tsaro suka ƙaddamar da samame a yankunan da ke kewaye da filin jirgin saman domin farautar sauran maharan da suka tsere.

Haka kuma, ta bayyana cewa dakarun ƙasar sun ƙwace ababen hawa da tarin makamai mallakin mayaƙan da ke iƙirarin jihadi, waɗanda ke ci gaba da kai hare-hare a sassa daban-daban na ƙasar.

Wannan ne karo na biyu da ake kai hari a filin jirgin saman Diori Hamani cikin wannan shekara, bayan wani makamancin harin da aka kai a watan Janairu, wanda ya haddasa fargaba a tsakanin mazauna Yamai.

A cikin ’yan watannin nan, hare-haren mayaƙan da ke iƙirarin jihadi sun ƙaru a babban birnin Nijar, lamarin da ya sa mahukunta suka fara rushe wasu gine-gine da ke kusa da filin jirgin saman, bisa zargin cewa maharan na amfani da su wajen shirya hare-hare.

Tun da safiyar Alhamis ne mazauna Yamai suka wayi gari da ƙarar harbe-harbe a yankin filin jirgin saman.

Rahotanni sun ce harbe-harben sun fara ne da misalin ƙarfe 6:00 na safe agogon ƙasar, inda aka shafe kusan awa guda ana jin su a yankin.

Wasu mazauna sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa an riƙa jin ƙarar harbe-harben daga kusa da ƙofar shiga filin jirgin saman.

Jamhuriyar Nijar ta shafe fiye da shekara goma tana fama da hare-haren ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi da ke kai wa jami’an tsaro da fararen hula farmaki.

A watan Janairun wannan shekarar ma, an kai wani hari a filin jirgin saman na Yamai, wanda ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin kaiwa.

Kamar ƙasashen makwabtanta na Burkina Faso da Mali, Nijar na ƙarƙashin mulkin soja bayan juyin mulkin da ya kawo ƙarshen gwamnatin farar hula.