Harin Damboa ya tilasta mutum dubu 15 yin gudun hijira zuwa Biu

Akalla mutum dubu 15 ne suka yi gudun hijira zuwa karamar Hukumar Biu sakamakon harin da ’yan kungiyar Boko Haram suka kai karamar Hukumar Damboa da ke Jihar Borno a karashen makon jiya.Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) a Arewa maso Gabas ce ta bayyana haka inda ta ce harin ’yan bindigar ya […]

Harin Damboa ya tilasta mutum dubu 15 yin gudun hijira zuwa Biu
Harin Damboa ya tilasta mutum dubu 15 yin gudun hijira zuwa Biu

Akalla mutum dubu 15 ne suka yi gudun hijira zuwa karamar Hukumar Biu sakamakon harin da ’yan kungiyar Boko Haram suka kai karamar Hukumar Damboa da ke Jihar Borno a karashen makon jiya.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) a Arewa maso Gabas ce ta bayyana haka inda ta ce harin ’yan bindigar ya tilasta mata da yara, kuma a yanzu haka suna zaune ne a wasu makarantu da wuraren da hukumar ta tanada musu kuma tana kokarin samar musu kayayyakin bukatun yau da kullum ta yadda za su samu saukin gudanar da rayuwarsu, kuma ta ce akwai wadanda suka samu raunuka da wadanda suke bukatar kulawar gaggawa da ta dauke su zuwa asibitoci don kulawa da su.
Tun maraicen ranar Alhamis din makon jiya ne ’yan Boko Haram suka kai hari a Damboa da ke da nisan kilomita 80 daga Maiduguri, har zuwa ranar Asabar suna ta kone-konen gidaje da muhimman wurare tare da kashe mutane.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa mazajen da suka tsira, sun bazama cikin daji suka rika kwana a kan itatuwa don tsira da rayukansu, a yayin da mata da yara suka zauna cikin firgici da tsoro har wayewar gari kafin su tsere zuwa wasu wuraren. Majiyar ta ce, maharan ba su bar wasu mata da yaran ba sai da suka kashe su.
’Yan bindigar sun kame garin Damboa suka kuma tayar da tutocinsu suna nuna cewa sun ci garin da yaki.
Wani da ya tsura daga garin da ba ya son a fadi sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa, “Mun ga ’yan bindigar sun shigo Damboa a motoci da babura masu yawa rike da miyagun makamai inda suka kwashe tsawon lokaci suna ta barna da kashe mutane ba ji ba gani.”
Jami’in Labarai na karamar hukumar, Sheriff Muhammed, ya tabbatar wa wakilinmu cewa bayan lafawar harin Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Zanna Umar Mustapha, ya bi hanyar Damboa daga Biu tare da jami’an tsaro inda suke rika kwasar mata da yaran da suka gudu suna kai su garin Biu, inda aka tanadar musu da sansani.
Aminiya ta samu labarin cewa jami’an tsaro da Sibiliyan JTF sun yi wa garin zobe, bayan harin da fitar ’yan Boko Haram daga garin aka kone akasarin gidaje da kasuwanni da makarantu da muhimman gine-ginensa.