Harin jiragen Isra’ila ba zai kawo karancin mai ba —’Yan Houthi

Kamfanin mai na Houthi ya tabbatar wa mazauna cewa akwai isasshen mai sannan ya umarci masu gidajen mai da kada su rufe su ko su kafara farashi.

Harin jiragen Isra’ila ba zai kawo karancin mai ba —’Yan Houthi

Mayakan Houthi sun sanar cewa harin bom da jiragen Isra’ila suka kai a  babbar tashar fitar da mai da ke yammacin kasar Yemen ba zai  haifar da karancin mai ba.

A ranar Lahadi ne jiragen Isra’ila suka yi ruwan bama-bamai a tashoshin samar da wutar lantarki da tashoshin jiragen ruwa a birnin Hodeidah da kuma Ras Issa da ke karkashin ikon ’yan Houthi.

Hare-haren sun lalata tashoshin wutar lantarki biyu da tashoshin jiragen ruwa guda biyu, kwana guda bayan mayakan Houthi sun yi ikirarin kai hari da makami mai linzami da jirgi maras matuki kan Isra’ila.

Tashar talabijin ta Al-Masirah ta Houthi ta ruwaito cewa, jiragen Isra’ila sun kai hare-hare a tashar jiragen ruwa da ke Hodeidah da tashar jiragen ruwa da ke Ras Issa, ciki har da babbar tashar fitar da mai.

Sun kuma lalata tashoshin wutar lantarki na Al-Katheeb da kuma Al-Hali, babbar tashar wutar lantarki ta Hodeidah, gaba daya, tare da kisan ma’aikata.

Kafar Al-Masirah ta ce an samu ma’aikata uku a karkashin baraguzan gini a masana’antar yayin da masu aikin ceto ke kokarin gano wasu mutane da suka makale.

Rundunar sojin Isra’ila a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce jiragen yakinta sun kai hari kan cibiyoyin ’yan tawayen Houthi a Hodeidah da kuma Ras Issa.

Da yake kawar da fargabar harin jiragen a Hodeidah zai haifar da karancin mai, kamfanin mai na Houthi ya fitar da wata sanarwar tabbatar wa mazauna yankunan da ke karkashinsa cewa akwai isasshen mai.

Kazalila ya umarci masu gidajen mai da kada su rufe su ko kuma su kafara farashi.

Harin ya zo ne kwana guda bayan da ’yan Houthi masu samun goyon bayan Iran suka yi ikirarin harba makami mai linzami a filin jirgin sama na Ben Gurion da ke Isra’ila.

Sun kuma sha alwashin kai irinsa da makami mai linzami nan gaba domin nuna goyon bayan Falasdinawa da matsa lamba ga Isra’ila ta kawo karshen yakinta a Zirin Gaza.

Tun a ranar 20 ga watan Yuli ne jiragen yakin Isra’ila suka kaddamar da hare-hare kan sansanonin ’yan Houthi da ke Hodeidah, inda suka kashe mutane 90 tare da raunata wasa 90.

Isra’ila ta kaddamar da hare-haren ne kwana guda bayan ’yan Houthi sun kai hari da jirgi mara matuki a Tel Aviv, suka kashe mutum guda tare da jikkata wasu da dama.

Tun a watan Nuwamba ’yan Houthi suka harba daruruwan makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan da kuma Isra’ila, da kuma jiragen ruwa na kasuwanci da na soji a tekun Bahar Maliya da sauran tekuna da ke gabar kasar Yaman, a wani mataki na goyon bayan al’ummar Palasdinu.

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra