Harin Jirgi: Shettima ya nemi afuwar al’ummar Sakkwato
Shettima, ya buƙatci al’ummar Sakkwato su ci gaba da bai wa sojoji sahihan bayanan da za su inganta aikinsu.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya nemi afuwar al’ummar Jihar Sakkwato, kan mutuwar mutum 10 a harin da sojoji suka kai wa ’yan ta’addan Lakurawa a Ƙaramar Hukumar Silame.
Lamarin ya faru ne a ranar 25 ga watan Disamba, 2024, inda wasu suka jikkata.
- Hatsarin jirgin sama ya hallaka mutum 122 a Koriya Ta Kudu
- Tinubu na ɓoye wa ’yan Najeriya gaskiyar halin da ƙasa ke ciki — Sule Lamido
Rundunar Sojin Saman Najeriya, ta bayyana cewa an kai harin ne bayan samun bayanan sirri, amma za su binciki mutuwar mutum 10.
A cikin wata sanarwa, Shettima, ya bayyana damuwa kan lamarin, inda ya bayyana hakan a matsayin abu ne mai wahala da ba kasafai ke faruwa ba a yaƙi da ’yan ta’adda.
Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu tare da yin kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa sojoji goyon baya ta hanyar ba su sahihan bayanai don inganta aikinsu.
Hakazalika, ya tabbatar wa ’yan Najeriya da cewa gwamnati za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa don kawo ƙarshen ta’addanci da tabbatar da tsaron al’umma.
A wani ɓangare, Shettima ya kai ziyara Jihar Jigawa, domin yi wa Gwamna Umar Namadi ta’aziyya kan rasuwar mahaifiyarsa da ɗansa.
Gwamnan na Jigawa ya rasa mahafiyarsa da ɗansa cikin sa’o’i 24.