Harin jirgin Abuja-Kaduna: Yadda muka tsallake rijiya da baya
Yadda Rahma Abudlmajid da sauran matafiya suka ka mutuwa ra’ayal aini a jirgin kasa.
A bangaren talaka komai ya tsaya babu abin da yake da tsaro sai jirgin kasa mai zarya tsakanin Abuja da Kaduna, shi ma wannan ba don talakan ake ba shi tsaro ba, na fi zaton ya sami nasa tagomashin ne saboda manyan jami’an gwamnati da ke tafiya a cikinsa.
Dole dai, da yake talakan Najeriya dan rakiya ne, haka muke bin wannan jirgi a gindi a gindi don mu isa inda za mu a cikin lumana, albarkacin kaza kadangare kan sha ruwa a kasko.
- ISWAP da Ansaru ne suka dasa ‘bom’ a titin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna
- Najeriya A Yau: Harin Jirgin Kasa ya ja wa Najeriya asarar N25m a kullum
Tun da aka fara sufurin jirgin kasa ni da jirgin muke makwabtaka saboda katanga ce ke raba mu, na san dadinsa na kuma san dacinsa, na san daga lokacin da jirgin ya fara sanya fasinjan dare a cikin dimuwa saboda zai yi wuya a jera sati yana kai fasinjan karfe 6 Kaduna a cikin awa biyu.
Don haka ne ma na kudiri aniyar daina bin jingin daren tun bayan wata rana da na ji shi da kyar ya iso da misalin karfe 2 na dare.
A ranar Lahadin da ta wuce ina cikin wannan jirgi cikin zullumi saboda na lura da tagar da nake zaune kusa da ita na da alamar ko dai harbin bindiga ko kuma wani kwakkwaran makami mai saiti.
Na rika duban wannan tagar a tsorace. Me ya faru da ita? Yaushe abin ya faru? Yaya ba labari? Ni ma na gaji da labaran jirgin nan kawai na share zancen har muka iso lafiya.
“Rahma ki raba kanki da bin jirgin nan,” wannan wata kalma ce da wata kusa a gwamnati kuma aminiyata ta taba ja min kunne da ita, kuma ita ta rika kuda a kunnena a jiya da muke tsugune a kungurmin daji ba gaba ba baya, har na tsawon awa biyu da rabi kowa ya sallama wa rayuwarsa.
Na rika kallon sama ko zan ji gilmawar helikofta din nan da ke tasowa tare da jirgin saboda ba shi tsaro, kuma yake bai wa na cikin jirgin kwarin gwiwa.
Amma shiru sararin samaniya sai ungulu ke yawo da alamar an sha kashe mutane a wurin a bar musu nama.
Da farkon tsayawarmu bayan da wutar jirginmu ta dauke sannan ya yi wata tsayawa kamar mota ta yi wawan taka burki alamar ba lafiya, mun ga jami’an tsaro da bindigogi suna shawagi, amma kafin minti 30 muka neme su muka rasa sama ko kasa.
Shin wani salon kare rayuka ne ko na guduwa ne wa ya sani?
Mafi munin abin da za mu gani shi ne jirgi na dawowa daga Kaduna ba a hayyacinsa ba, ya sha harbi gaba da gefe, fasinja na tsaitsaye kamar ba kujera cikin matsanancin tashin hankali.
Duka suna cewa mu juya mu koma ana fashi a gaba, amma fa mu ba dama mu yi gaba ko baya domin namu jirgin ba shi da kai da zai yi ribas.
Fasinja suka rude wasu na kokarin neman hanyar da za su haike wa wancan jirgin da zai koma Abuja don ya cece su, amma ina, shi ma ta kansa yake.
Wasu suka debi jakunkuna suka kama gudu a daji don ceton kawunansu da kansu, musamman bayan ganin matukan jirgin sun kama hanyar tafiya neman dauki a gigice.
Abu daya da ya rage min da zai samar min da natsuwa shi ne tuna Maulidi da farincikin samuwar Annabi (SAW) don haka kawai na shiga aikin yawo tsakanin taragun jirgin ina salati ina sanya mutane dariya, ina kuma karyata labaran da na fi kowa sanin gaskiya ne don na lura akwai masu hawan jini kuma ya fara kawo hari, haka har Allah Ya kawo mana dauki inda jami’an jirgin suka dawo da kayan kwance kai don su jona shi a alkiblar Abuja.
Shawara uku da zan bai wa mahukumta
1 – Dole ne a dawo da ‘network’ kan hanyar jirgin saboda matsalar sadarwa ce ta kara dagula tsaro a jiya, domin da a ce su da kansu mahukumta jirgin na da kafar sadarwa ba za su tayar da wani jirgin a yayin da wanda ke kan hanya ya sha luguden wuta har sau biyu a jere ba.
2 – A sanya wa kowane jirgi kai biyu maimakon guda daya, domin zubar da daruruwan mu da jirgin ya yi a jiya ba zai faru ba da a ce yana da kai me dawowa tunda jirgi baya kwana kamar mota.
3 – A dawo da helikwaftoci din nan da ke shawagi a sama idan dai da gaske ne.
Shawarata ga talakawa, ita ce, idan ba a dauki mataki na gani da ido kan lamarin nan ba mu kaurace wa jirgin nan.
Hakika gwamnati ba ta da asara idan rayuwarmu ta shiga tasku, amma tana da asara idan jirginta ya kasa samar da kudin shiga sakamakon yajin da muka yi masa.