Harin jirgin kasa: Ba mu san ko ’yan ta’adda ba ne —Gwamnati

Babu tabbacin ko ’yan ta’adda ne suka tarwatsa titin jirgin kasan.

Harin jirgin kasa: Ba mu san ko ’yan ta’adda ba ne —Gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta da tabbaci cewa ’yan ta’adda ne suka tarwatsa titin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Hukumar Sufurin Jiragen Kasa ce ta sanar da hakan ta bakin Manajan Daraktanta, Fidet Okhiria, jim kadan bayan latata layin dogon da aka yi da nakiya a safiyar Alhamis.

Ya ce “Gaskiya ne an lalata titin jirgin kasan,” sai dai ya ce ba shi da tabbacin ko ’yan ta’adda ne suka yi aika-aikan, amma hukumar na gudanar da bincike a kan lamarin.

A cewarsa, hukumar na zargin bata-gari ne suka lalata titin jirgin kasan, la’akari da yadda ake samun karuwar satar karafan jirgin kasa a baya-bayan nan.

Manajan Daraktan Hukumar ya yi watsi da rahotannin da ke cewa ’yan ta’adda ne suka kai harin a kan layin dogon da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna.

Ya ci gaba da cewa “layin dogon ya samu matsala amma muna kokarin gyarawa, kuma zuwa yau (Alhamis) da yamma za mu iya ci gaba da gudanar harkokinmu.

“Jirginmu ya zo daga Kaduna zuwa Abuja yau da safe amma daga baya dole muka dakatar da zirga-zirga saboda barnar da aka yi, sai mun gama gyara,” kamar yadda ya bayyana.

Ya kara da cewa hukumar na aiki tare da hukumomin tsaro domin tsaurara matakan tsaro a hanyar jirgin na Abuja zuwa Kaduna.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu