Harin jirgin soji a Zamfara: Ya kamata a biya mu diyya —Iyalai

Iyalan fararen hula da harin jirgin soji ya rutsa da su bisa kuskure a kananan hukumomin Maradun da Zurmi a Jihar Zamfara sun bukaci gwamnati ta biya su diyya.

Harin jirgin soji a Zamfara: Ya kamata a biya mu diyya —Iyalai

Jirgin Sojin Saman Najeriya

Iyalan fararen hula da harin jirgin soji ya rutsa da su bisa kuskure a kananan hukumomin Maradun da Zurmi a Jihar Zamfara sun bukaci gwamnati ta biya su diyya.

Mutum 15 ne suka mutum, wasu tara suka samu munanan raunuka a hare-haren jiragen sojin da ke yaki da mayakan Lakurawa.

A ranar 11 ga watan nan na Janairu ne jirgin sojin saman Najeriya ya jefa wa fararen hula bom a kauyen Gidan Kara da Malikawa da Sakida da  Kakidawa da Tungar Labbo da ke kananan huukumomin biyu, bayan su yi kuskuren dauke cewa ’yan ta’adda ne.

Daga cikni wadanda harin ya ritsa da su har da jami’an tsaron al’umma na Jihar Zamfara (CPG).

Muhammad Aminu, wanda dan uwa ne ga daya daga cikin jami’an tsaron da aka jikkata a harin, mai suna Babangida Ibrahim, ya roki Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Zamfara su biya diyyar wadanda abin ya shafa.

Aminu ya ce, “Daga cikin mamatan akwai wadanda su ke kula da ’yan uwansu don haka akwai bukatar gwamanti ta biya iyalan nasu diyya.

“Ya kamata ta biya diyyar wadanda suka rasu ta biya kudin asibitin wadanda suka samu raunim, saboda jami’an gwamnati ne suka kai hari, kuma wadanad abin ya fada a kansu aikin taimakon gwamanti suke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Saboda haka ya kamata gwamnati ta duba ta yi abin da ya kamata ga iyalansu.”

“Idan ta biya to shi ken nan, idan ta ki kuma za mu bar ta da Allah, amma ba za mu taba yafewa ba.

“Tawagar gwamnatin Zamfara da kuma sojojin sama sun zo sun yi alkawarin taimaka wa iyialan, amma har yanzu jiya muke.”

Wani wanda kaninsa ya rasu a harin, wanda ya nemi kar a bayyana sunansu ya ce, “Ina jira in ga me gwamnati za ta yi. Sun dai zu sun yi mana tambayoyi, amma ba mu san abin da hakan zai haifar ba.

“Alhamdulillah, a wurin tsaron rayukan al’umma ’yan uwanmu suka rasu, kuma muna alfahi da hakan. Amma duk da haka shugabanni su sani cewa idan aka yi watsi da wannan batu, to zai sanyaya gwiwwar masu son shiga su taimaka wajen yakanr ’yan bindiga.

“Babu wanda zai sayar da ransa ba tare da adalci ba, don haka nake ba gwamnati shawara a jiha da tarayya su duba yiyuwar biyan diyya ga iyalan, saboda rashin hakan zai iya karya gwiwar masu niyyan taimaka mata a yaki da ’yan bindiga, ba a Zamfara ba kadai, har da sauran wurare.”

Malama Halima Idrisa, matar Idrisa Agima ta ce an yi watsi da wadanda suka jikkata, babu wani tallafi daga gwamnati a kowane mataki.

Ta ce “Yanzu kwana biyar da faruwar wannan abu amma babu wani abu na taimako da muka samu daga gwamnati. Dan abin da muka tara muke kashewa wajen jinyar ’yan uwanmu. Muna so gwamnati ta kawo mana dauki.”

A nasa bangaren mashawarcin gwamnan Zamfara kan yada labarai, Alhaji Mustapha Jafaru Kaura ya ce fara maganar biyan diyya a yanzu ya yi sauri, domin “kwamitoci biy da gwamnatin Zamfara da Rundunar Sojin Sama suka kafa na kan aiki.”

Ya ce ya kamata a yi hakuri sai kwamitocin sun kammala bincike kamar yadda aka yi lokacin da irin haka ta faru a wasu jihohi, sannan a san irin taimakon da gwamnati za ta bayar.