Harin Jirgin yaki: Sojoji na bincike kan kisan fararen hula a sansanin ’yan ta’addan Kaduna

Rundunar Sojin Saman Najeriya ta fara bincike kan harin da jiragenta suka kai kan maboyar ’yan ta’adda a Jihar Kaduna

Harin Jirgin yaki: Sojoji na bincike kan kisan fararen hula a sansanin ’yan ta’addan Kaduna

Babban Hafsan Sojin Saman Najeriya Air Marshal Hasan Abubakar

Rundunar Sojin Saman Najeriya ta ce za ta fara bincike mai zurfi kan harin da jiragen yaki suka kai maboyar ’yan ta’adda a Jihar Kaduna.

Shaidu sun sanar da Aminiya cewa hare-ahren sun kashe wasu mutanen kauyen da ba su ji ba ba su gani ba a ranar Juma’a.

Aminiya ta ruwaito a ranar Litinin cewa mazauna kauyen Jika da Kolo da ke Yadin Kidandan a Karamar Hukumar Giwa a jihar suna zargin cewa wadanda harin ya rutsa da su sun hada da masallata 23 a wani masallaci da wasu a wata kasuwa.

Amma da yake mayar da martani, Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar, Guruf Kyaftin Kabiru Ali, ya bayyana cewa wurin ya yi kaurin suna wajen zama sansanin ’yan ta’adda sama da shekaru 2.

Guruf Kyaftin Ali ya bayyana cewa nasarar da aka samu, ko shakka babu zai taimaka matuka wajen rage yawan ’yan fashin daji da ake kaiw a mutanen da ba su ji ba ba su gani ba hari a Jihar Kaduna da kewaye.

Ya ce, “rundunar na da labarin zargin an samu fararen a harin da aka samu ta sama a wani kan ’yan ta’adda suka kai a Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.

“Harin da aka kai ta sama a wurin ya samo asali ne daga sahihan bayanai daga majiyoyi masu inganci, da kuma sa ido kan wuraren da aka kai harin.

“Wurin ya yi kaurin suna a matsayin yankin ’yan ta’adda sama da shekaru biyu kuma nasarar da aka samu ta sama ko shakka babu za ta taimaka matuka wajen rage ’yan taa’adda da hare-haresnu a kan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba a jihar Kaduna da kewaye.

“Duk da haka, rundunar ba ta dauki wadannan zarge-zargen da wasa ba

“A halin yanzu ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike don gano gaskiyar lamarin da nufin sanar da jama’a a kan lokaci,” in ji shi.

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro