Harin Jos: ‘Mun kai rahoton motar da bam din ya tashi ga ’yan sanda’
Daya daga cikin wadanda suka tsallake harin bam din da ya tashi a Jos wanda ya halaka sama da mutum 118 a ranar Talatar da ta gabata, ya ce sun kai rahoton motar ga ’yan sanda ganin an ajiye ta ba tare da sun san wanda ya ajiye ta a wurin ba, amma ba su […]

Daya daga cikin wadanda suka tsallake harin bam din da ya tashi a Jos wanda ya halaka sama da mutum 118 a ranar Talatar da ta gabata, ya ce sun kai rahoton motar ga ’yan sanda ganin an ajiye ta ba tare da sun san wanda ya ajiye ta a wurin ba, amma ba su yi wani kokari don bincikar abin da take dauke da shi ba.
Mutumin mai suna Kabiru Idris ya shaida wa Aminiya cewa da suka ga motar kirar J5 da safe, sai suka kai rahoto ga ’yan sanda wadanda suka cire lambarta, amma ba su yi wani kokari na su binciki abin da take dauke da shi ba.
“Mu da muke kasuwar mun lura da J5 din sai muka sanar da ’yan sanda cewa ba mu san masu motar ba, amma sai kawai suka cire lambar motar suka ce lokacin da mai ita ya zo ya je ya same su,” inji shi.
Ya kara da cewa, “Yanzu ga irin abin da ya same mu, duba duk mutanenmu sun mutu. Me muka yi da za a yi mana wannan? Mu talakawa ne masu bin doka da oda da suke neman abin da za su ci.
A ranar Talata da misalin karfe 2:30 zuwa 3:00 ne garin Jos ya hadu da harin tagwayen bama-bamai a daidai lokacin da babbar kasuwar Jos ke ci gaba da hada-hada, harin da ya ci rayukan mutum 118 tare da raunata da dama a babbar kasuwar da ke kusa da tsohon Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH).
Wadannan hare-haren bam na Jos, an gudanar da su ne ta hanyar sanya su a cikin motoci biyu aka zo aka ajiye su a wurin da suka tashi.
Wadanda abin ya faru a kan idonsu sun shaida wa wakilinmu cewa bam na farko ya tashi ne cikin motar kirar J5 da misalin karfe 2:30, yayin da bam na biyu ya tashi a cikin wata Toyota da misalin karfe 3:00 .
Shaidun sun shaida wa wakilinmu cewa a lokacin da bam na farko ya tashi ya rutsa da mutane da dama da suka hada da ’yan kasuwa da masu wucewa a motoci da masu tafiya a kasa. Suka ce ana cikin aikin ceto wadanda fashewar bam din ta rutsa da su ne, sai kuma aka ji wani bam din ya sake tashi a cikin daya motar da take kusa da wurin.
Tashin bam na biyu ya fi na farko barna domin ya fi rutsawa da mutane dama, kuma shaidun sun ce an ajiye motocin ne a wurin tunda sanyin safiyar ranar.
Masu aikin ceto sun rika dibar sassan jikin mutanen da harin bama-bamai ya rutsa da su da suka hada da hannuwa da kafafu suna durawa a cikin buhunhuna, a yayin da aka rika dibar wadanda suka ji munanan raunuka ana kaiwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos da ke kusa da kuma Asibitin kwararru na Jihar Filato da Asibitin Jankwano.
A lokacin da lamarin ya faru, hankulan al’ummar garin ya tashi, inda mutane suka yi ta guje-guje a cikin gari.
Kafin faruwar hare-haren bam din mutanen Jos sun yi shekara biyu suna zaune lafiya, bayan fama da rikice-rikicen addini da kabilanci a shekarun baya.
A cewar ko-odinetan Hukumar Agajin Gaggawa ta kasa (SEMA), Muhammad Abdulsalam zuwa dare a ranar Talatar sun gano gawarwaki 118. Ya ce za a iya samun kari musamman ganin akwai gine-ginen da ake tunanin sun rushe da mutane a wurin. Ya ce sun dauki mutum 56 da suka samu raunuka zuwa asibiti.
Tunda farkon a taron manema labarai Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Filato, Mista Chiris Olakpe ya ce mutum 46 ne suka rasu, a yayin da mutum 45 suka samu raunuka a hare-hare. Kwamishinan ya kuma ce wannan hari ne na ’yan ta’adda.
Tuni shugabannin siyasa da na addini suka yi Allah wadai da harin na Jos, wanda ya zo bayan kwana biyu da kai hari a Kano wanda ya ci mutum tara.